Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mako Daya Kafin Zaben Shugaban Kasar Amurka Clinton da Trump Sun Kara Kaimi


Hillary Clinton ta Democrat da Donald Trump na Republican
Hillary Clinton ta Democrat da Donald Trump na Republican

Ana kimanin mako daya a yi zaben shugaban kasa na Amurka, kuma yayinda ra’ayoyin jama’a ke nuna cewa ‘yan takaran na kut da kut da juna a wurin goyon bayan jama’a,Hillary Clinton ta Democrat da Donald Trump na Republican sun kara kaimin a yakin neman zabensu, suna kai ziyara a jihohi da sai dole dan takara ya lashe su kafin a ce ya yi nasaarar lashe zaben shugabancin kasar.

Dan takarar Republican Donald Trump jiya Talata da dare a jihar Winsconsin ya gargadi yan Democrat da suka riga suka kada kuri’unsu a shirin kuri’ar sammako, da su koma su canja kuru’unsu tun da yake dokar jihar tana bada daman yin hakan.

Donald Trump ya maimaita wannan kiran a wasu jihohi inda doka ta baiwa mutane damar su chanja kuri’unsu ko bayan sun riga sun jefa su, idan suka ji cewa basu son abinda suka zaba daga farko.

Sanarwar da darektan hukumar binciken manyan laifuka ta FBI James Comey ya yi a waccan mako cewar hukumarsa tana sake duban sakwannin email na lokacin da Clinton take sakatariyar harkokin wajen Amurka, ya ba Trump wani sabon karfi saboda ana ganin abokiyar karawar tasa bata da gaskiya.

A watanni hudu da suka wuce ne Comey ya sanar cewar hukumar FBI ta riga ta duba baki dayan sakwannin email na Clinton kuma ta gano babu wani abinda zai sa a gabatar da ita gaban shara’a a ciki.

Da take kempen jiya Talata a jihar Florida, Clinton tace sanarwar Comey ana gabda zabe a ranar takwas ga wannan watan Nuwamba wani abin damuwa ne, inda kuma tace wulakancin da Donald Trump ke yiwa mata da irin kalamansa a kansu, abin takaici ne.

Shima shugaba Barack Obama jiya ya wuni a jihar Ohio yana yi wa Hillary Clinton kyamfen, da yake jihar na cikin muhimman jihohi da kowane dan takara ke kwadayin samun lashe su.

Ra’ayoyin mutane na baya bayan nan sun nuna ana samun kusanci sosai tsakanin Clinton da Trump, wadanda ko bayansu akwai wasu ‘yan takaran shugaban kasa na wasu jam’iyyu da suka hada da Gary Johnson na jam’iyyar Libertarian da Jill Stein ta Green Party.

XS
SM
MD
LG