Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Sun Yi Kira Ga Samun Sabbin Sauye-sauye A ECOWAS/CEDEAO


ECOWAS
ECOWAS

Masana da kwararru sunyi nazarin cewa kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO, na bukatar sake tsari da sauye-sauyen da za su yi daidai da manufofin kasashe mambobinta.

AGADEZ, NIGER - Wannan nazarin na zuwa ne bayan gaza katabus wajen daukar mataki akan sojojin da suka yi juyin mulki a wasu kasashe mambobin kungiyar ta ECOWAS da aka dade ana daukar ta a matsayin wadda ta fi ci gaba a Afirka.

Sai dai wasu na ganin abin yanzu ba haka ya ke ba sakamakon juye-juyen mulki da sojoji suka yi a kasashe daban-daban na yankin wanda ya nuna cewa kungiyar ba ta da hurumi ko karfi wajen magance matsalolin yankin.

Masana irin su Abdourahamane Dikko sun bayyana cewa ya zama wajibi idan kungiyar tana son samun galaba ta nuna kishin Afirka da kuma samar da wasu sauye-sauye da za su yi daidai da manufofin kasashen yankin. Ya ce ta haka ne kawai kungiyar za ta iya samun amannar kasashen yankin.

Masanan na ganin sabon shugaban kasar Senegal na da kusancin ra’ayi da kasashen Nijar, Mali da kuma Burkina Faso, kuma fahimtar sa da gwamnatocin kasashen uku ka iya sa shi neman sauye-sauye a kungiyar ta ECOWAS a cewar Usman Dumbia wani manazarcin siyasar kasa da kasa a Mali.

Ya ce ya zama wajibi a samar da wasu sabbin sauye-sauye a cikin kungiyar ta ECOWAS domin sake dawo da kasashen nan uku cikin kungiyar tare da sake tunani na yin gaba-da-gaba da kasashen Yamma ta yadda kungiyar za ta sami martaba da daraja a idanun duniya, na iya fada aji kuma haka na iya yiwuwa.

Jinkiri da da sakaci na kin hobbasa daga bangaren kungiyar ECOWAS din wajen ciyar da yankin yammacin Afirka gaba na daga cikin dalillan zubewar martabar ta don haka masanan ke ganin akwai bukatar a sake lale a yi nazari akan abubuwa da yawa.

Ana ganin tsakanin kasashen kungiyar yammacin Afirka wasu na tufka wasu kuma na warware ra’ayin tafiyar da ita, masanan na ganin da ba don haka ba da tuni kungiyar ta samar da mafita akan makomar kasashen Nijar, Mali da kuma Burkina Faso.

Saurari cikakken ragoto daga Hamid Mahmud:

Masana Sun Bukaci Sabbin Sauye-sauye A Cikin ECOWAS-CEDEAO.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG