Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Fama Da Cutar HIV Sun Koka a Jihar Naija


Masu fama da HIV suna sauraron bayani
Masu fama da HIV suna sauraron bayani

Masu fama da cutar HIV da ke arewacin Najeriya sun yi amfani da ranar daya ga watan Disamban nan da majalisar dinkin duniya ta ware domin tunawa da masu cutar wajen bayana halin ko in kular da ake nuna masu a jihar Naija.

Masu fama da cutar HIV da ke arewacin Najeriya sun yi amfani da ranar daya ga watan Disamban nan da majalisar dinkin duniya ta ware domin tunawa da masu cutar wajen bayana halin ko in kular da ake nuna masu a jihar Naija.

Jihar Naija na da adadin mutane dubu dari uku da hamsin da ke fama da cutar HIV. Wani sugaban kungiyar masu fama da cutar HIV a jihar, Sani Chrisopher Marcus, ya bayana cewa mutane da dama masu fama da cutar HIV suna bukatan kula da kuma taimako mai muhimanci, musamman ta wajen samun abinci da sauran su.

Ita kuma sakatariyar kungiyar mata masu zama da cutar HIV, Angela Layiki, ta fadi cewa ya kamata masu kiwon lafiya da gwamnati gabaki daya su rika sa su a cikin ayukan su na kiyaye wanan cutar.

Uwar gidar gwamnan jihar Naija, Hajiya Jumai Babngida Aliyu, ta baiwa masu cutar gudumuwar kayan abinci kuma ta bayana cewa gwamnati tana abin da ya kamata kuma tana iyaka kokarin ta a wajen kiyaye cutar HIV.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG