Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-Zanga Sun Gwabza Da 'Yan Sanda A Najeriya


Masu zanga-zanga sun kona tayu a kan tituna lokacin gangamin nuna kin jinin janye tallafin farashin man fetur a Lagos, talata 3 Janairu 2012.
Masu zanga-zanga sun kona tayu a kan tituna lokacin gangamin nuna kin jinin janye tallafin farashin man fetur a Lagos, talata 3 Janairu 2012.

An yi zanga-zanga a Kano da Lagos da kuma Kwara inda 'yan kwadago suka ce 'yan sanda sun kashe mutum guda

Masu zanga-zanga a Najeriya sun yi arangama da jami'an tsaro a lokacin da ake nuna tunzurin kin jinin matakin da gwamnati ta dauka na kawar da wani shiri mai farin jini ga talaka na janye tallafin farashin man fetur.

Kungiyoyin kwadago sun shirya gangami a sassa da dama na birnin Lagos, amma wasu masu nuna fusata sun kona tayu da tarkace a kan tituna, suka kwashi ganima a gidajen sayar da mai, suka kuma ja kunnen masu gidajen man da kada su sayar da shi a kan sabon farashin da yayi mummunan tashi.

A Kano dake arewacin najeriya ma an gudanar da zanga-zanga, yayin da a Jihar Kwara ta yammacin kasar Kungiyar kwadago ta NLC ta ce 'yan sanda sun harbe suka kashe mutum guda a lokacin da ake nuna kin jinin janye tallafin man fetur din. 'Yan sanda a Jihar sun musanta wannan ikirarin.

Wannan tallafin farashin mai na daya daga cikin abubuwa kalilan da talakawan Najeriya, wadanda ba su samun abinda ya wuce naira 300 a rana, suke cin moriyarsu daga arzikin man fetur na kasar.

Jami'an gwamnatin Najeriya dai su na ci gaba da bayyana amfanin janye tallafin farashin. Shugaba Goodluck Jonathan yace kawo karshen tallafin farashin zai samarwa da gwamnati kudaden samar da kayayyaki da kyautata rayuwar jama'a.

Wasu hotunan zanga-zangar ta yau a Lagos:

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG