Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Fama Da Miyagun Iri A Karamar Hukumar Karu Da Ke Kusa Da Abuja – James Thomas


Shugaban Karamar Hukumar Karu, James B.Thomas
Shugaban Karamar Hukumar Karu, James B.Thomas

Shugaban karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa Mr. James B. Thomas ya ce har yanzu yankin na fama da 'yan ta'adda da kuma daukar bakuncin 'yan gudun hijira kasancewar sa magamar jama'a daga ciki da wajen Najeriya.

Wannan karamar hukumar da ke jikin babban birnin tarayya Abuja na cikin kananan hukumomi da ke da mafi yawan jama'a a Najeriya.

Yara 'yan gudun hijira sun ta shewa yayin da Muryar Amurka ta ziyarci a kauyen Luvu da ke karamar hukumar ta Karu don ratsawa can lungun su yayin kai mu su kayan agaji da wata kungiyar tallafi ta Khadija ta yi, da ya jawo hankalin gwamnatin jihar Nasarawa don kawo mu su dauki da kare su daga bata gari.

Yara 'Yan Gudun Hijira A Kauyen Luvu da ke Karu A Jihar Nasarawa
Yara 'Yan Gudun Hijira A Kauyen Luvu da ke Karu A Jihar Nasarawa

James B. Thoms wanda a baya ya taba ayyana dokar ta baci don samar da tsaro, ya ce an samu saukin kalubalen amma da sauran rina a kaba “duk abun da baka tsammani Boko Haram da sauran su akwai a wannan yankin, shi ya sa mu ke cewa kowane kauye su kafa ‘yan bangar su. Rundunar soja ta 77 da ke Keffi da DSS na taimaka ma na.”

Kwamishiniyar ayyukan jinkai ta jihar Nasarawa, Princess Margret Itake Elayo, ta ce za su ci gaba da zuba ido kan lungunan yankin don kai daukin gaggawa.

Commissioner of Humanitarian Affairs Nasarawa State Margaret Itake Elayo
Commissioner of Humanitarian Affairs Nasarawa State Margaret Itake Elayo

Daya daga cikin iyaye mata 'yan gudun hijira daga Goza a jihar Borno, Malama Ladi Haruna, ta bayyana cewa sun tsallake kadarkon mutuwa kafin isowa yankin, amma su na fama da karancin abinci da ababen more rayuwa.

Malama Ladi ta ce "mu na bukatar abinci, makaranta don yaran mu da asibiti. Mun kai 600 a nan kuma mun bar gida sanadiyyar kisan gillar Boko Haram."

'Yan Gudun Hijira A Kauyen Luvu da ke Karu A Jihar Nasarawa
'Yan Gudun Hijira A Kauyen Luvu da ke Karu A Jihar Nasarawa

Hajiya Adama Ahmed Mai Agogo da ke jagorantar tallafin ta yi alwashin kara himma wajen kai dauki ga wadanda isa wajen su ma babbar dawainiya ce “asibiti da makaranta duk za mu yi kokarin ganin an bude a sansanin.”

Akasarin ma'aikata da ke aiki a Abuja na zaune ne a yankin na Karu don saukin muhalli da albashin su zai iya daukar nauyi.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG