Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Uku Sun Rasa Rayukansu A Ambaliyar Ruwa A Jamhuriyar Nijar


Wata unguwa inda aka yi ambaliyar ruwa a Najeriya
Wata unguwa inda aka yi ambaliyar ruwa a Najeriya

Ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya a Maradi Jamhuriyar Nijar ya yi sanadin rusa gidaje dari biyar da sittin da biyu kimanin iyalai dubu biyu kuma suka rasa matsugunansu.

Ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya a Maradi Jamhuriyar Nijar ya yi sanadin rusa gidaje dari biyar da sittin da biyu kimanin iyalai dubu biyu kuma suka rasa matsugunansu.

A cikin hirarsu da Halima Djimroa, Kassoum Mouctar, shugaban majalisar da’ira birnin Maradi ya bayyana cewa, an tafka ruwa kimanin milimita kusan dari, bayanshi kuma aka yi wani kimanin milimita zuwa hamsin da shida, da arba’in da bakwai wanda ya haddasa barna wanda ya maida unguwar Maza da Jika tamkar korama.

Shugaban Majalisar da’irar birnin Maradin ya bayyana cewa, yanzu haka galibin mutanen wannan unguwa kimanin gidaje dari zuwa dari da hamsin suna zaune a azuzuwan makarantu dake kusa da unguwar.

Shima a nasa bayanin Tijjani Inouwa wani mazaunin Damagaran yace an shafe kimanin sa’a guda ana tafka ruwa a wani lokacin kuma da kankara wanda bisa ga cewarshi, tunda yake bai taba ganin irin wannan ruwan ba.

Kawo yanzu mutune uku suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan, yayinda ake ci gaba da tantance irin asarar da ruwan ya janyo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG