Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutun Hudu Sun Mutu A Hadarin Jirgin Ruwa A Jihar Kebbi


Wani kwale-kwale ya kife a karamar hukumar mulkin Jega a jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya a daren Litinin.

Rahotanne sun bayyana cewa hatsarin kwale-kwalen mai dauke da mata 10 da matuki, yayi sanadiyyar mutuwar mata 4, yayin da sauran 6 kuma ba'a sami ganinsu ba.

Shugaban hukumar ba da agajin gaugawa ta jihar Kebbi, Alhaji Sani Dododo wanda ya tabbatar da haka a zantawarsa da wakilinmu Muhammad Nasir, ya ce za'a ci gaba da lalube domin gano sauran mutanen 6.

Ya bayana cewa da misalign karfe takwas da rabi na daren Litinin ne suka sami labarin da ya tabbatar da afkuwar hadarin. A cewar sa jirgin ya taso ne daga wani gari da ake ce mishi Gehoru.

Kamar yadda Alhaji Sani Dododo ya shedawa wakilin namu, "nan take aka shiga aikin ceto, kuma an sami gano gwarwakin mata hudu a locacin da muke ba da wannan rahoto."

An alakanta wanna hadari daya afku da abaliyar ruwa sanadiyyar mamakon ruwan sama da ake samu a ‘yan kwanakin nan.

Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta sha kira ga mutane da su kauracewa hanyar ruwa saboda gudun asarar da ambaliya kan iya hadasawa.

Idan za’a iya tunawa tun farkon daminar bana masana yanayi suka ba da sanarwa yiwuwar ruwan sama mai yawa da zai iya haddasa ambaliya mai karfin gaske.

In a related development, Two persons were confirmed dead and another missing after a fishing boat with seven passengers capsized in Ikorodu

A wata makamanciyar wannan kuma, an tabbatar da rasuwar mutum biyu sanadiyyar nutsewar wani jirgin ruwan masunta a Ikorodu ta jihar Lagas.

Hadarin ya auku ne da misalign karfe bakwai na yammacin Litinin a Offin Ibeshe sa'adda igiyar ruwa mai karfin gaske ta kifar da kwale-kwalen.

A bayanin da hukumar sufurin ruwa ta jihar Legas (LASWA) ta bayar, jirgin da ya tashi daga Makoko, ya na dauke da mutum bakwai ciki har da kananan yara biyu.

Shugaban hukumar LASWA, Oluwadamilola Emmanuel ya ce dukan fasinjojin ba sa sanye da rigar kariya wato life jacket a locacin da hadarin ya auku.

“Inquiries reveal that the fishing boat which was clearly operating outside its fishing capability and therefore not equipped with necessary safety gadgets for passengers ferry operation carried the occupants who are all related and headed to Offin for a relative’s funeral.

Ya ce "binciken da aka yi ya nuna cewa jirgin kamun kifin bai da muhimman na’urorin amfani da kariya ga fashinjojin, domin dukkaninsu ‘yan uwan juna ne danke hanyarsu ta zuwa jana’izar wani dan’uwansu.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG