Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NDLEA ta cafke mutane uku dauke da hodar ibilis a sansanin 'yan gudun hijira dake Maiduguri


'Yan gudun hijira, Jihar Borno
'Yan gudun hijira, Jihar Borno

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA ta cafke wasu mutane uku da hodar ibilis da ake kira koken a daya daga cikin sansanin 'yan gudun hijira dake cikin birnin Maiduguri

Shugaban hukumar NDLEA na jihar Borno Barrister Joseph Ona shi ya shaidawa manema labarai a wani taron fadakarwa akan illar shan miyagun kwayoyi da suka gudanar a birnin Maiduguri.

Yace yawaitar ta'ammali da miyagun kwayoyi abu ne mai tada hankalin gaske ganin yadda ake yawan kama tabar wiwi da hodar iblis da ake kira koken.

Da yake magana akan wadanda suka kama a sansanin 'yan gudun hijira da hodar iblis yace nan ba da jimawa ba zasu gurfanar dasu a gaban shari'a. Baicin mutanen uku da suka kama da koken a sansanin 'yan gudun hijiran sun kuma kama wasu 16 dake yin anfani da tabar wiwi duk a sansanin.

A cikin garin Maiduguri sun kama wani mutum wanda ya boye tabar wiwi mai nauyin kilo dari da goma sha biyu a cikin gidansa lamarin da ya nunawa hukumar cewa ana hada-hadar tabar wiwi a tsakanin al'umma.

Barrister Joseph Ona yace ba zasu yi kasa a gwuiwa ba wajen ganin sun rage irin wadannan miyagun mutane dake bata tarbiyan al'umma.

Abun takaici, hukumar ta kama wasu 'yan Civilian JTF guda uku da suka fito daga garin Kareto na karamar hukumar Mobar da motar Civilian JTF ta karamar hukumar suna dauke da wasu layu da makamai tare da tabar wiwi a cikin motar.

Shugaban kananan dillalan masu sayarda magunguna a jihar Borno ya yi bayani akan mahimmancin taron. Sun shirya taron ne domin wayar da kawunan jama'a akan illar da shan kwaya ke yiwa matasa. Maganin da yakamata a sha domin warkaswa matasan suna sha domin su bugu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG