Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Sa Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Sayar Wa Mali Da Man Diesel A Farashi Mai Sauki


Gen. Abdourahmane Tchiani, Niamey, Niger
Gen. Abdourahmane Tchiani, Niamey, Niger

An cimma wata yarjejeniyar da a karkashinta jamhuriyar Nijar ta amince ta sayar wa kasar Mali lita million 150 na man diesel akan farashi mai sauki.

NIAMEY, NIGER - Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta ayyana shirin gina wata matatar mai a yankin yammacin kasar da nufin sassauta wahalhalun jama’ar kasashen kawancen AES a fannin man fetur.

Ministan man fetur na Nijar Mahaman Moustapha Barke ne ya sanar da wannan kudiri na gina matatar man fetur a jihar Dosso dake tazarar km 139 a kudu maso gabashin Yamai babban birni jim kadan bayan wata ganawa a birnin Bamako da shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mali Kanal Assimi Goita.

Ya ce a halin yanzu motocin dakon man kan yi lodi ne a km kusan 900 da Yamai to idan aka yi sabuwar matata a Dosso dake a tazarar km 139 da Yamai abu ne da zai takaita hanya. Za a yi sabuwar matatar a Dosso takanas domin bai wa kasashen AES damar daukan mai.

Kakakin gamayyar kungiyar direbobi ta UTTAN Gamatche Mahamadou na ganin abin tamkar wata hanya karfafa hadin kan kasashen Sahel ne.

Ministan ya jagoranci tawagar Nijar a wurin bukin saka hannu kan wata yarjejeniya a tsakanin kamfanin dillancin man metur wato SONIDEP da a daya gefe kamfanin makamashi da ruwan sha EDM Mali wacce a karkashinta Nijar ta amince ta saida wa kamfanin na Mali lita million 150 na man diesel akan farashi mai sauki.

Wannan yarjeniya na zuwa a wani lokacin da Kasar Mali ke cikin matsanancin halin karancin wutar lantarki abin da ka iya zama wani matakin samar da mafita.

A hirar shi da Muryar Amurka, Choguel Maiga Firaiministan gwamnatin rikon kwaryar Mali ya ce wannan yunkuri na dangantaka da Nijar ta yi zai bai wa EDM damar inganta ayyukan samar da wuta ga abokan cinikayyarsa.

To sai dai su ma ‘yan kasa sun fara bayyana bukatar ganin hukumomi sun yi yadda arzikin man Nijar zai amfani jama’ar kasa.

A yayin wani taron da ya gudana a watan fabrerun da ya gabata a birnin Yamai, gwamnati ta amince ta fara sayar wa kasashen AES har ma da Togo da Chad man fetur dinta cikin farashi mai rangwame da zummar taimaka masu tunkarar tsadar man da ake fuskanta a mafi yawancin kasashen Afrika.

Nijar wacce ta fara tace manta a matatar SORAZ dake Zinder a 2011 na hangen soma cin kasuwar danyen mai ta duniya daga watan Mayun gobe inda ake sa ran kaddamar da ayyukan bututun hadin guiwa da CNPC China wanda aka shimfida daga rijiyoyin Agadem jihar Diffa zuwa tashar jirgin Ruwan Seme a Jamhuriyar Benin.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Nijar Ta Sa Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Sayar Da Man Diesel Kan Farashi Mai Sauki Wa Mali.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG