Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Palasdinawa sun mika wa Majalisar Dinkin Duniya takardun neman wakilci a kotun kasa da kasa.


Zauren Majaliar Dinkin Duniya
Zauren Majaliar Dinkin Duniya

Palasdinawa sun mikawa Majalisar Dinkin Duniya takardun neman wakilci a kotun kasa da kasa, domin su samu sukunin cajin kasar Isira'ila da aikata laifuffukan yaki.

Palasdinawa sun gabatar wa Majalisar Dinkin Duniya takardun neman samun wakilci a kotun kasa da kasa ICC, matakin da zai basu damar neman a caji kasar Isira'ila da laifin aikata laifuffukan yaki.
Jiya Juma'a Jakadan Palasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansur da wani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya suka tabbatar cewa an mika wadannan takardun a hedikwatar Majalisar.
Mr Mansor yace matakin yana da muhimmanci wajen neman ayi adalci ga laifuffukan da ake zargin an aikatawa Palasdinawa. Haka kuma yace Palasdinawa zasu nema adalci daga kotun ICC dangane da laifuffukan da aka aikata a fafatawar da aka yi a Gaza a bara.
Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas shine ya rattaba hannu akan takardun, bayan da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yayi watsi da daftarin kudurin da aka gabatar a farkon wannan makon, daya baiwa Isira'ila wa'adin shekaru uku ta janye daga yankunan Palasdinawa data mamaye bayan yakin da suka gwabza a alif dari tara da sittin da bakwai da kuma neman kafa kasar Palasdinu.
Prime Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu yayi barazanar maida martanin da bai baiyana ba, akan bukatar Palasdinawa na neman wakilici a kotun ICC.

XS
SM
MD
LG