Wani sabon bincike da wasu masana suka gudanar akan rikicin mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya ya gano wasu daga cikin dalilan da suka sa matasa da yawa shiga kungiyar Boko Haram.
Dr. Abba Sadik, wani sanannen dan jarida da ke birnin Paris, na daga cikin wadanda suka gudanar da binciken, ya ce sun yi nazari kan abubuwa da dama da suka ja ra’ayin matasa shiga kungiyar Boko Haram kuma sun gano cewa da yawa daga cikin su ba don addini suka shiga ba, wasu kuma sun shiga kungiyar ne bisa tunanin zasu samu arziki saboda sun dauke ta kamar wata sana'a tunda basu da abin yi.
Ya kara da cewa wasu da suka shiga kungiyar da sunan addini amma daga baya suka gane cewa kungiyar Boko Haram ba addini ta ke bi ba kuma suka so su ja da baya an kashe su.
Game da wadanda rikicin Boko Haram ya fi shafa, Dr. Sadik ya ce mafi akasari mata da yara ne suka fi jin jiki. Mata da yawa sun zama gwamraye, yara kuma sun zama marayu. Wasu mazan kuma ba su san halin da matansu ke ciki ba tun bayan da aka sace su.
A nashi bangaren Zanna Hassan Bugoma, ya na ganin cewa a kowane lokaci jama’a kan kalli ayyukan ta’addanci da ‘yan kungiyar ke kai wa ba tare da la’akari da bangaren gwamnati ba, kuma ga dukkan alamu babu niyar kawo karshen wannan yakin yanzu.
Duk da cewa shugaban kasa da jami'ansa na iya kokarin su wajen kawo karshen rikicin, akwai bukatar gwamnati ta kara daukar matakai da suka dace don kawo karshen ayyukan ta’addanci a Najeriya da ma makwabtanta baki daya.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina daga N’Djamena a kasar Chadi.
Facebook Forum