Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Bayyanar Alkali Ya Kawo Tsaiko A Shari’ar Zambar Naira Bilyan 6 Da Milyan 900 Da Fayose Ke Fuskanta


An ce mai shari’a aneke yayi wani balaguron aiki, abinda ya sabbaba daga cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 1 ga watan yuli mai zuwa.

WASHINGTON DC - A yau Alhamis, an samu tsaiko a shari’ar halasta kudaden haram da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose saboda rashin bayyanar alkali, Mai Shari’a Chukwujekwu Aneke na Babbar Kotun Tarayya dake jihar Legas.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ce ta gurfanar da Fayose a bisa zarginsa da zambar naira bilyan 6 da milyan 900 da kuma halasta kudaden haram.

A ranar 22 ga watan Oktobar 2018 aka fara gurfanar da Fayose, gaban Mai Shari’a Mojishola Olatotegun, tare da kamfaninsa mai suna, “Spotless Investment Ltd, a bisa tuhume-tuhume 11 dake da nasaba da laifuffukan zamba da halasata kudaden haram.

A ranar 24 ga watan Oktoban 2018, Fayose yaki amsa laifinsa bayan da aka karanto masa tuhume-tuhumen: inda aka bada belinsa akan kudi naira milyan 50 da shedu da suma zasu biya hakan.

An sake gurfanar da Fayose gaban Mai Shari’a Cchukwujekwu Aneke a ranar 2 ga watan Yulin 2019, bayan da aka janye karar daga gaban Mai Shari’a Olatotegun, biyo bayan korafin da hukumar efcc ta gabatar akan alkalin.

Har ila yau ya sake kin amsa laifinsa inda aka sahale masa cigaba da belin da aka bashi tunda fari, sannan aka sake dage sauraron karar.

Tuni Hukumar EFCC ta sake gabatar da karar tasa gaban Mai Shari’a Aneke kuma tana cigaba da gabatar da shedu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG