Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rick Santorum Ya Janye Daga Neman A Tsaidashi Dan Takarar Shugabancin Amurka


Tsohon Senata Rick Santorum tareda iyalansa a taron manamen labarai inda ya sanar ya jnaye.
Tsohon Senata Rick Santorum tareda iyalansa a taron manamen labarai inda ya sanar ya jnaye.

Senata Rick Santorum daya daga cikin wadanda ke kokarin ganin jam’iyar Republican ta tsayar dashi dan takarta na shugaban kasa ya janye daga wannan bege. To amma kuma yace zai ci gaba da yin aikin ganin jam’iyarsa ta kada shugaba Obama a zaben shugaban kasa.

Tsohon Senata Rick Santorum, daya daga cikin wadanda ke kokarin ganin jam’iyar Republican ta tsayar dashi dan takarta na shugaban kasa ya janye daga wannan bege. To amma kuma yace zai ci gaba da yin aikin ganin jam’iyarsa ta kada shugaba Obama a zaben shugaban kasa.

Jiya Talata Rick Santorum ya bada wannan sanarwa a Gettysburg jihar Pennslyvania, kwana daya bayan an sallami ‘yarsa mai suna Bella daga asibiti inda aka yi mata jinya.

Ya godewa magoya bayansa. Shi dai Santorum ya janye ne mako guda bayan ya sha kaye a hannun tsohon gwamnan jihar Massachusetts Mitt Romney, a zaben tsayar da dan takara a jihohi uku da aka yi.

Da, tsohon senatan, ya kwallafa rai kan zaben fidda dan takara da za yi a jiharsa ta Pennsylvania ranar 24 ga watan nan,da nufin samun nasara,da hakan zai zaburadda yakin neman zabensa bayan kayen da ya sha a baya bayan nan.

Amma ko da ya lashe jihar Pennsylvania, Santorum sai ci gaba da kasancewa can baya ga Romney wajen yawan wakilan zaben ‘yan takara, domin zama mutuminda jam’iyyar zata tsayar takarar shugabancin kasa.

Romney ya yabawa Santorum kan yadda ya gudanar da yakin neman zabe, ya kira shi cikakken abokin takara, kuma muhimmin mutum a harkokin siyasar Amurka.

Baya ga Mitt Romney, yanzu sauran tsohon kakkaki Majalisar Wakilai Newt Gingrich da kuma dan Majalisar Ron Paul a wannan takara.

XS
SM
MD
LG