Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Riek Machar Ya Sake Samun Mukaminsa A Sudan Ta Kudu


Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, ya sake nada tsohon mataimakin sa Riek Marchar, da ya ci gaba da zama mataimakinsa, wannan ko bai rasa nasaba da ganin an kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru biyu ana yi a kasar ba.

Shugaba Kiir, ya bayyana dokar nada Riek Marcher ne jiya alhamis, domin yin hakan zai cike daya daga cikin manya-manyan sharuddan da ada aka gitta a cikin watan Agusta na shekarar da ta gabata amma kuma aka ki yi.

Yanzu dai wannan ya mayar da martaban shugaban kasar inda yake tun farko. kafin yaki ya barke tsakanin magoya bayan shugabannin biyu, lokacin da shugaba kiir ya fatattaki mataimakin nasa a cikin watan Disambar shekarar 2013.

Da yake wa Muryar Amurka bayani, a babban birnin Masar, Mercher yace yana mai cike da farin ciki na wannan sake nada shi da akayi a matsayin mataimakin shugaban kasar su.

Yace da farko yana yiwa shugaba Kiir godiya na daukar wannan matakin domin ganin cewan yanzu za a cimma duk wasu sharuddan da aka gindaya.

Marcher yace yanzu basu da ko wace irin hujja na kin aiwatar da wadannan sharuddan

Ita dai kasar Sudan da kudu ita ce sabuwar kasa a duk fadin duniya wadda ta samu ‘yancin ta a daga kasar Sudan a cikin shekarar 2011.

XS
SM
MD
LG