Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Bincike Kan Gawar Mohbad, Ana Zaman Jiran Sakamako


Mohbad (Hoto: Facebook/MohBad official)
Mohbad (Hoto: Facebook/MohBad official)

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya ba da umurni a hukunta duk wanda ya taka wata rawa da ta kai ga mutuwar mawakin.

Hukumar ‘yan sandan jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce ta kammala bincike kan gawar mawaki Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.

Mawakin mai shekaru 27 ya rasu ne a ranar 12 ga watan Satumba cikin wani yanayi mai cike da rudani da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Kashegarin rasuwarsa aka yi jana’izarsa, wani abu da shi ma ya janyo ka-ce-na-ce.

Sai dai a ranar Alhamis ‘yan sanda suka tono gawar Mohbad don gudanar da bincike bayan da aka yi ta samun korafe-korafe har daga mawaka abokansa.

“Rundunar ‘yan sandan Najeriya na sanar da jama’a cewa, an kammala binciken gawar Mr. Mohbad cikin nasara.

“Da zarar sakamakon binciken ya fito za mu sanar da jama’a.” Sanarwar da ‘yan sandan Najeriyar ta fitar a ranar Alhamis ta ce.

Dubban mutane ne suka yi zanga-zanga a sassan Najeriya don nuna fushinsu kan yadda mawakin na Afrobeat ya mutu cikin wani yanayi mai cike da alamar tambaya.

A birnin Legas, an yi wani taro na zaman jimami a ranar Alhamis inda aka ga matasa suna tattaki suna kiran da a bi wa mawakin kadinsa.

Rahotanni sun ce fitattun mawaka irinsu Davido, Zlatan da Falz sun halarci taron zaman jimamin yayin da ake gudanar da bincike kan gawar Mohbad.

Mohbad ya rasu ne bayan da aka garzaya da shi wani asibiti bisa wani rashin lafiya da ba a sani ba.

Bayanai sun yi nuni da cewa, an yi wa mawakin wata allura a lokacin da aka kai shi asibitin.

Daga nan kuma rai ya yi halinsa.

Mohbad, wanda a da mawaki ne karkashin kamfanin Malians na fitccen mawaki Naira Marley, ya fito idon duniya da wakokinsa irinsu ‘Ponmo, Peace, Ask About Me’ da sauransu.

A bara ne ya kuma fice daga kamfanin bisa wasu dalilai da har yanzu ba a fayyace ba.

A ranar Talata Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu, ya ba da umurnin a hukunta duk wanda ya taka wata rawa da ta kai ga mutuwar mawakin.

Saurari rahoton Babangida Jibril:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG