Antonio Gueteres yace maida martini bayan rikici ya auku ya kanainaiya aikin Majalisar Dinkin Duniya shekara da shekaru. Yace lokaci yayi daya kamata Majalisar ta dauki matakan rigakafin barkewar rikici domin tabbatar da zaman lafiya.
Mr Gueterres yace tilas rigakafi ya zama abinda za’a rika yi a kowane lokaci. Muhimmin mataki ne na rage wahala da jama’a suke sha domin cimma burorinsu ta rayuwa.
Haka kuma sabon sakataren na Majalisar Dinkin Duniya yayi kira ga kasashen duniya da su maida hankali wajen amfani da dabarun diplomasiya domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.