Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shugaban Koriya Ta Kudu Moon Jae, Yace A Shirye Yake Ya Kai Ziyara Koriya ta Arewa


A yau Laraba ne aka rantsarda Moon bayan da ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a kasar jiya talata.

Sabon zababben shugaban kasar Koriya Ta Kudu, Moon Jae, ya fada a yau Laraba cewar a shirye yake ya ziyarci makwabciyarsu, Koriya Ta Arewa, kuma ya nemi sasantawa da China da Amurka akan rikicin ajiye garkuwar makami mai linzami da Amurka tayi a Koriya Ta Kudu.

A yau ne Moon Jae yake wannan kalaman, jim kadan bayanda ya dauki rantsuwar kama aiki a birnin Seoul sakamakon nasarar da yayi ta lashe zaben da akayi jiya Talata.

Hukumar zaben Koriya Ta Kudu ta tabbatar da nasararsa da samun kashi 41 cikin 100 na kuri’u, inda ya lallasa Abokin takararsa mai ra’ayin rikau Hoon Joon-pyo wanda ya sami kashi 24 cikin 100 na kuri’un yayinda Mai matsakaicin ra’ayi Ahn Cheol-soo ya sami kashi 21 cikin 100 na kuri’un.

Zaben ya shiga cikin tarihi sakamakon yawan mutanen da suka fito domin kada kuri’a, wanda aka ce ya kai kashi 77 cikin 100 na masu jefa kuri’a na kasar, wanda ya biyo bayan yanayin rikicin da ya shafi tsohuwar shugabar kasar Park Geun-hye da ake zargi da sa hannu a cikin wata damfara ta miliyoyin daloli, sakamakon haka mutane suka yi gagarumar zanga zanga wacce ta tilasta Majalisar kasar ta tsige ta daga mukaminta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG