Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UNGA: Tinubu Ya Yi Jawabi A Ranar Farko Da Aka Bude Mahawara A Taron Kolin MDD A New York


Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu

Shugabannin kasashe sama da 30 ne suka yi jawabi jiya da ke zama ranar farko da aka bude mahawara a taron kolin MDD na cikon 78 a birnin New York 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce guguwar juyin mulki da ta taso a Afrika ba komai ba ne illa yunkurin gyara matsalolin da aka dade ana fama da su.

Ya ce; "Ya kamata mu tabbatar da dimokaradiyya a matsayin hanya mafi inganci ga ‘yancin al’umma da muradunsu. Juyin mulkin soji ba daidai ba ne, kamar yanda ake samun rashin adalci a shugabancin farar hula, amma wannan iska ta juyin mulki da ke kadawa a Afrika ba ta na nufin bude hanyar juyin mulki ba ne illa gyara matsalolin shekara da shekaru. Ku bari mu zurfafa tunani."

Taron UNGA
Taron UNGA

"Amma a kan batun Nijar mu na tattaunawa ga shugabannin sojan a matsayina na shugaban ECOWAS ta yanda za a kafa gwamnatin dimokaradiyya da za ta magance matsalolin siyasa da tattalin arziki da kasar ke fuskanta, da ma batun tashin hankalin ‘yan ta’adda da ke kara dagula al’amura a yankinmu."

Shugaban Tinubu ya yi kira ga kasashen duniya da su yi aiki tare da kasashen Afrika a matsayin abokan hulda wurin bunkasa tattalin arziki amma ba wanda ake kallo masu neman tallafi ba.

Wani batun da shugaban ya tabo shi ne na sauyin yanayi da shugabanni da dama suka yi magana a kai.

Tinubu ya nuna illolin da sauyin yanayi ya yi wa Najeriya tare da buga misali da kasar Libya inda ambaliya ta kashe dubban mutane. Ya ce kasashen Afrika za su yaki sauyin yanayi amma dole su yi hakan bisa adalci, kafin cimma nasarar aikin, wannan gangami na bukatar sa himma a fannin tattalin arziki.

Antonio Guterres
Antonio Guterres

Yayin bude taron, babban sakataren MDD Antonio Guterres shi ma ya bayyana takaici a kan rashin daukar kwararan matakai kan batun sauyin yanayin da hakan yake haddasa manyan ibtila’o'i da ke haddasa asarar rayuka kamar ambaliyar da aka gani a kasar Libiya. Ya ce ko yanzu da muke magana ana samun gawarwaki a kogin meditariniya inda hamshakan attajirai ke shakatawa a kananan jiragen ruwansu. Ya ce ambaliyar garin Darna na kasar Libiya ba komai ba ne illa ambaliya ce ta rashin daidaito ta rashin adalci da kuma ta rashin maida hankali wurin magance matsalolin tsakaninmu.

Cyril Ramaphosa
Cyril Ramaphosa

Shugaban Afrika Ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya fada a yayin jawabinsa cewa dole ne kasashe masu arzikin masan’antu su bada gagarumar gudunmuwa wurin dakile batun sauyin yanayi. Ya ce Afrika na dumama cikin gaggawa, saboda ita ce keda 17 cikin yanayi 20 mafi tsananin zafi a duniya, Afrika ba ta da hannu wurin gurbata yanayi amma ita ce ta fi shan wahalar sauyin yanayin.

Ramaphosa ya kuma tabo batun fadada kwamitin sulhun MDD domin wasu kasashen Afrika su samu wakilcin dindindin a kwamitin.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG