Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata Ayogu Eze Ya Mutu Yana Da Shekaru 66 A Duniya


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Tsohon dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Enugu ta Arewa kuma tsohon shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Ayogu Eze, ya rasu. Sanata Ayogu, ya rasu yana da shekaru 66 a duniya.

Ayogu, wanda ya kasance a Majalisar Dokoki ta kasa tsakanin 2007 zuwa 2015, ya rasu ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, a wani asibitin Abuja bayan ya yi fama da rashin lafiya.

A tsawon shekaru takwas da ya yi a Majalisar Dattawa, Eze ya kasance mamba a kwamitin tsara kundin tsarin mulki da gyara wanda ya yi wasu sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Bayan sake zabensa a Majalisar Dattawa a 2011, an nada shi shugaban kwamitin ayyuka na Majalisar Dattawa.

Sanata Ayogu, ya kuma yi aiki a matsayin memba na kwamitocin harkokin ‘yan sanda, tsare-tsare na kasa, sufurin ruwa da kuma al’amuran gwamnatin tarayya.

An haifi Sanatan ne a ranar 23 ga Nuwamba 1958, an zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Enugu ta Arewa a jihar Enugu, inda ya karbi mulki a ranar 5 ga Yuni, 2007.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG