Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lokaci Ya Yi Na Kawo Karshen Yaki a Sudan


Sudan
Sudan

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta ce: "An shafe kwanaki 100 kenan tunda fada tsakanin Sojojin Sudan da Dakarun Ba da Agajin Gaggawa ya barke, kuma a wannan lokacin, tashe-tashen hankula na rashin fahimta sun haifar da wahalhalu da ba a taba tsammani ba."

“Miliyoyin mutane sun rasa matsugunansu... An harbe fararen hula a kan titi. An mayar da yara marayu, an tilasta su shiga kungiyoyi, ana cin zarafinsu. An yi wa mata fyaden wulakanci. Yaki ya toshe taimakon jin kai - abinci, ruwa, magunguna, da sauran abubuwan da ake bukata - zuwa ga mutanen da ke cikin matsananciyar bukata. Akwai rahotanni masu sahihanci da ke nuna cewa dakarun gaggawa da kawayenta na ci gaba da cin zarafi a yammacin Darfur."

Ambasada Thomas-Greenfield ta bayyana cewa, Amurka ta yi Allah wadai da wadannan ta'asa da aka ruwaito, wadanda ke nuni da kisan kiyashin da aka yi a Darfur a shekara ta 2004.

"Kuma mun damu matuka game da hadarin karin rikici a arewaci da tsakiyar Darfur. Musamman, ta wani rahoto da aka samu na dakarun gaggawa da na haɗin gwiwa a kusa da El Fasher, wanda ke yin barazana ga mutanen da ba Larabawa ba a yankin. Mun damu matuka da rahotannin da ba a tabbatar ba na wasu masu dauke da makamai a Sudan sun hana mutane barin yankunan Darfur domin su samu su tsere, ciki har da kan iyakar kasar zuwa Chadi."

"Muna da alhakin ... ba kawai daukaka 'yancin ɗan adam ba, amma kare su," in ji Ambasada Thomas-Greenfield. "Don haka, dole ne dukkanmu mu bukaci bangarorin da su bi hakkinsu a karkashin dokar jin kai ta kasa da kasa game da kare fararen hula." Amurka da kawayenta na kasa da kasa suna kira ga bangarorin da su gaggauta ajiye makamansu.

A halin da ake ciki dai, Amurka a matsayinta na kasa daya tilo mai bayar da agajin jin kai ga al'ummar Sudan, tana kokarin tallafawa miliyoyin mutanen da suka rasa matsugunansu da kuma wasu kusan miliyan daya da suka yi gudun hijira zuwa kasashe makwabta.

Matsalolin aikin gwamnati da ire-irensu sun kawo cikas ga ayyukan agaji, in ji Ambasada Thomas-Greenfield:

"Muna kira ga hukumomin Sudan da su gaggauta amincewa da ba da biza ga ma'aikatan jinkai, da ba da damar zirga-zirgar kayayyakin jinkai da na ma'aikata a duk fadin Sudan, da kuma saukaka shigo da kayayyakin jin kai."

“Dole ne mu yi kira ga sojojin Sudan da dakarun gaggawa da su kawo karshen zubar da jini da kuma kawo karshen wahalar da al’ummar Sudan ke ciki. Babu wata hanyar soji da za ta iya magance wannan rikicin,” in ji Ambasada Thomas-Greenfield. "Kuma zaman lafiya ba zai iya jiran gobe ba."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG