Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekih Khalil Ya Lashe Amansa Akan Manjo Al-Mustapha


Manjo Hamza al-Mustapha
Manjo Hamza al-Mustapha

A wata huduba da ya taba yi Sheikh Sanusi Khalil ya taba cewa Manjo Hamza Al-Mustapha yana tarbiyar da matasa domin gwamnatin tarayya tayi anfani dasu wurin aikata kisan kai lamarin da ya sa shi Al-Mustapha ya garzaya kotu kai kara

Biyo bayan wani taron sulhu a karkashin shugabancin Dr Ahmed Mahmud Gumi, Sheikh Sanusi Khalil yace ya janye zargin da yayi na cewa shi Manjo Hamza yana tarbiyar da matasa domin su kashe duk wanda gwamnati ta ga suna yi mata barazana.

Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya ya zanta da Sheikh Sanusi Khalil akan taron sulhun da kuma sakamakonsa. Yace ranar Alhamis da ta gabata aka yi taron kuma ya bada goyon baya ga duk abun da aka cimma a taron.

An zauna a karkashin jagorancin Dr Ahmed Mahmud Gumi. Bisa ga bayanan da Manjo Hamza Al-Mustapha yayi ya bayyana cewa baya horas da kowa tarbiyar kashe wadanda gwamnatin tarayya take ganin suna yi mata barazana. Manjo Hamza bashi da hannu wajen horas da matasa domin su kashe mutane. Bisa ga bayanan, Sheikh Khalil yace waccan magana da yayi akan Manjo Hamza Al-Mustapha ya janyeta. Gaskiyar magana yanzu ita ce Manjo Hamza yana tare da al'umma yana yaki da cin zalunci a kasar kuma yana bada irin nashi gudunmawa.

Wakilinmu ya tambayi Sheikh Khalil shin baya jin janye maganar zata sa masu binsa su soma dari-dari da shi. Sai ya kada baki yace "shi yana kara godiya ga Allah da ya kaddara wannan abu" Yace karar da Manjo Al-Mustapha ya kai ta zama rahama gareshi. Yace kafin zaben 2011 Allah ya sa yayi bayanan wasu abubuwa kuma babu wanda bai bayyana ba. Yace idan an gabatar da abubuwa ashirin ya zama daya ne kawai ya zama kuskure kamata yayi shi ya ji tsoron Allah ya fito ya janye maganar.

Dangane da ko sabili da tsoron kada kotu ta daureshi ne yasa ya janye maganar Sheikh Khalil yace kowa nada daman ya fadi ra'ayinsa akan maganar. Addu'ar da zai yi shi ne Allah ya haskaka zukatan irin wadannan mutanen. Kuma tun da shi Manjo Al-Mustapha yayi bayani kuma ya yadda da sulhun da aka yi to ai magana ta kare.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:07:31 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG