Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Me Ya Sa 'Yansandan Nigeriya Ke Yawan Aiwatar da Hukuncin Duka Kan Mutane


ADAMAWA, 'Yansandan jihar sun yiwa wani dalibi Kabiru mugun duka. Yanzu ransa na hannun Allah
ADAMAWA, 'Yansandan jihar sun yiwa wani dalibi Kabiru mugun duka. Yanzu ransa na hannun Allah

Tambaya da Kabiru Ahmed ya yiwa 'yansanda ta kaiga lakada mashi dan karen dukan da ya kwantar dashi a asibiti, rai hannun Allah lamarin da ya sa ana tambaya shin 'yansandan Najeriya nada ikon bugun mutum ko su maida kansu kotu su aiwatar da hukumci?

'Yansandan Jimeta ne suka kai samame a wata unguwa da nufin cafke wasu matasa dake shaye-shaye amma hakansu bai cimma ruwa ba saboda matasan sun sulale.

Amma wani matashi dan makaranta mai suna Kabiru Ahmed ya tambayesu dalilin zuwan 'yansandan unguwarsu da kuma kamen da suke yi. Wannan tambaya ce ta harzuka 'yansandan suka lakada mashi dan karen duka da ya kusa daukan ransa. Bayan sun yi masa duka kuma sai suka kaishi caji ofis dinsu.

Kabiru yanzu ya kwashe wata guda a asibiti amma har yanzu bai san inda yake ba. Saboda yanayin da Kabiru ke ciki da halin karya doka da 'yansandan Najeriya ke yawan yi ya sa kungiyoyin kare hakkin bil Adama da shugabanni sun bukaci babban sifeton 'yansandan Solomon Arase ya kafa kwamitin bincike yayinda wasu 'yan fafutika ke barazanar zuwa kotu.

Onarebul Lawal Garba dan majalisar wakilai dake wakiltar Yola ta kudu da Yola ta arewa da kuma Gire ya bukaci al'ummar Jimeta da su yi hakuri su kuma kwantar da hankalinsu domin ana bin kadun batun. Yace abun da ya faru ba shi ne na farko ba. Yace akwai wani Bala da 'yansanda suka taba yi masa duka har suka kasheshi.

Onarebul Garba yace a matsayinsa na kasancewa lauya da kuma zama dan majalisa zai bada shawarar a samu lauya ya rubuta korafi zuwa babban sifeton 'yansandan, kuma a bi lamarin cikin tsanaki tare da kaucewa karya doka kamar yadda 'yansandan Jimetan suka yi. Yace zasu bi doka su kwatowa Kabiru hakkinsa.

Shi ma shugaban kungiyar kare al'ummar Adamawa Alhaji Useni Gambo Bello Nakura wanda ya taimaka wajen kwantar da hankulan matasan yankin yace ba wannan ba ne karin farko da ake zargin 'yansanda da aikata ba dede ba inda suke wuce gona da iri.

Kakakin 'yansandan jihar DSP Usman Abubakar ya musanta cewa 'yansanda sun yiwa yaron duka. Yana cewa wai rami ne yaron ya fada yayinda yake gudu daga 'yansandan.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00
ADAMAWA, 'Yansandan jihar sun yiwa wani dalibi Kabiru mugun duka. Yanzu ransa na hannun Allah yana kwance a asibiti
ADAMAWA, 'Yansandan jihar sun yiwa wani dalibi Kabiru mugun duka. Yanzu ransa na hannun Allah yana kwance a asibiti

XS
SM
MD
LG