Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Saka Wani Bangaren Kayan Soji Laifi Ne a Najeriya?


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Najeriya kasace da ta yi kaurin suna wajen zarge-zarge cin zarafin bil adama da jami'an tsaro ke yi idan aka la'akkari da rahotannin da kungiyoyi kare hakkokin bil adama da dama suka sha fitar a baya.

Koda yake, hukumomin na Najeriya sun sha musanta ire-iren wadannan zarge-zarge.

A 'yan kwanakin nan an samu wasu sojoji da suka nakadawa wani mutum nakasashe duka saboda rahotannin dake nuna cewa ya saka kaya mai launin kayan soja.

Wannan lamari ya faru ne a birnin Onitsha dake jihar Anambra a kudu maso gabashin Najeriya, kuma ya ja hankulan mutane da dama bayan da wani hoton bidiyo da ya fita a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna yadda sojojin suka yi ta dukan mutumin.

Bayanai dai sun nuna cewa tuni aka cafke wadannan sojoji da suka aikata wannan aika-aika, kuma rundunar sojin Najeriya ta ce za a hukunta su.

Muhawarar da ta barke a yanzu ita ce shin ko mutum ya karya doka idan mutum ya saka wani sassan kayan jami'an tsaro musamman na sojoji?.

Saurari rahoton daya daga cikin wakilanmu na Abuja, Nasiru Adamu El hikaya ya hada domin jin wannan amsa:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

XS
SM
MD
LG