Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba AmurkaYa Yi Alkawarin Tallafawa Wadanda Guguwar Sandy Ta Durkusar


Shugaba Barack Obama ya rungunme wata da guguwar Sandy ta shafa
Shugaba Barack Obama ya rungunme wata da guguwar Sandy ta shafa
Dan takarar shugabancin Amurka na jami’iyyar Republican Mitt Romney ya koma yakin neman zabe jiya laraba, bayan dan jinkiri da aka samu sakamakon mahaukaciyar guguwar da tayi mummunar barna a yankuna dake gabashin Amurka.

Shugaban Amurka Barack Obama har yanzu yana ci gaba da maida hankali baki daya kan wannan bala’I har ma ya kai ziyarar ganema idonsa irin ta’adin da guguwar Sandy tayi, a jihar New Jersey.

Bayan ziyarar da yayi tare da gwamnan jihar Chris Chrisitie, shugaban yayi magana da manema labarai inda ya bayyana cewa, “Kamar yadda aka sani muna fadawa cikin mawuyacin hali, duk da haka muna mikewa nan da nan, dalilin da yasa muke farfadowa shine muna tallafawa juna, bama yarda mu kyale wani a baya.”

Gwamna Chrisitie, babban bako mai jawabi a babban taron kasa na jam’iyyar Republican da aka yi bana, kuma babban mai sukar lamirin gwamnatin shugaba Obama ne, duk da haka Gwamnan ya yabawa Mr. Obama kan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka dangane da wannan bala’I.

“ Bani da kalamai da zasu bayyana irin godiyata ga shugaban kasa saboda irin damuwa da tausayawa jiharmu da al’umarta da ya nuna”.

Ana sa ran shugaban na Amurka zai koma fagen yakin neman zabe yau Alhamis, inda zai yada zango a jihohin Wisconsin, Nevada, da kuma Colorado, jihohi da suke cikin wadanda ake yiwa lakabin mazari, saboda ba a san inda suka karkata ba.
XS
SM
MD
LG