Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Goodluck Jonathan Ya Gabatar Da Sunayen Ministocinsa


Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Daga cikin sunayen da shugaban na Najeriya ya gabatarwa da majalisar dattijai don neman amincewarta har da wasu tsoffin ministocin.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya tura sunayen mutane 34 da yake son nadawa ministoci zuwa majalisar dattijan kasar domin neman amincewarta. A yau talata shugaban majalisar dattijan, David Mark, ya karanta jerin sunayen ga ‘yan majalisa, amma ba a bayyana mukaman da ake son ba kowanne cikinsu ba.

Wasu daga cikin wadanda ake son ba ministocin sun hada da tsohon ministan kudi Olusegun Aganga da tsohon ministar man fetur Deziani Alison-Madueke.

Majiyoyin gwamnati sun ce akwai rahotannin cewa Mr. Jonathan yayi magana da manajin darektar Bankin Duniya ta yanzu Ngozi Okonjo-Iweala kan yiwuwar komawarta cikin gwamnatin, koda yake ba sunanta cikin jerin da aka gabatar yau talata. Okonjo-Iweala ta rike mukamin ministar kudi a tsohuwar gwamnatin Olusegun Obasanjo a Najeriya.

Majiyoyin gwamnati sun ce ana ci gaba da tattaunawa, amma kuma tana neman da a ba ta iko fiye da tsohon ministan kudin kasar.

XS
SM
MD
LG