Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban kasar Girka suna neman kara zaftare kudin da gwamnati ke kashewa


Shugabannin kasar Girka
Shugabannin kasar Girka

Shugabannin kasar Girka sun sake yin kira tare da gargadi dangane da matsayin tattalin arzikin kasar

Shugabannin kasar Girka sun sake yin wani sabon kira tare da gargadi, yayinda ake shirin kada kuri’ar da zata yanke hukunci kan ko kasashen turai zasu sake ceto kasar daga durkushewa ta wajen sake bata rance.

Shugaban jam’iyar ‘yan gurguzu George Papandreau da takwaranshi na jam’iyar New Democracy Antonis Samaras sun yi kira ga ‘yan majalisa yau da su goyi bayan sabon zaftare kasafin kudin, da cewa, basu da zabi.

Papandreus ya yi gargadi da cewa, gaza amincewa da matakan tsuke bakin aljihun zai jefa kasar cikin hakin ni ‘yasu.

A nashi bangaren kuma, Samaras ya gargadi ‘yan jam’iyarshi da cewa, ba za a amince da salon siyasar neman zabe ba.

Ana kyautata zaton kada kuri’a kan tsuke bakin aljihun ne gobe lahadi. Membobin kungiyar Tarayyar Turai sun bukaci karin zaftare kudin da gwamnatin kasar Girka ke kashewa kafin a bata wani sabon bashin dala biliyan 172 domin ta iya sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.

Tilas ne Girka ta biya bashin dala biliyan goma sha tara dake kanta watan gobe. Firai Minista Lucas Papademos ya shaidawa majalisar zartaswar kasar jiya Jumma’a cewa, mutuncin kasar zai zube har kasa idan ta gaza biyan wadanda suke binta bashi.

XS
SM
MD
LG