Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Iraqi Haider Al-Abadi Ya Bada Sanarwar Fara Yaki


 Haider al-Abadi
Haider al-Abadi

Dakarun kasar Iraqi da Amurka sun kaddamar da wani babban shiri a yau lahadi domin Kakkabe tsagerun Da’esh daga rabin yammacin Mosul

Wannan ya kasance wani sabon shafi bayan watanni hudu da aka kwashe ana tafka fada domin kwato ikon birnin na biyu mafi girma a kasar.

An tabbatar da yakin na yammacin Mosul zai zama mafi wahala tun da aka fara yakin, sakamakon yammacin birnin ta Kogin Tigris nada tsofafin lunguna kuma akwai Dubunnan daruruwan fararen hula dake zaune a wajen, wadanda aka cewa su buya.

Iraqi ta tabbatar da an yanta Gabashin Mosul a watan da ya gabata amma yan kungiyar Da’esh sun ci gaba da kai hare hare a wuraren. Awanni bayan an bayyana sabon shirin , yan kunar bakin wake suka afkawa kungiyar yan banga da masu goyon bayan gwamnati yan sunni a gabashin Mosul.

Firaminista Haider Al-Abadi ya bada sanarwar fara wannan yaki ne a gidan talabijin na jihar, inda ya bayyana cewa sojojin gwamnati na kutsawa domin yanta al’ummar Mosul daga musgunawar yan kungiyar Da’esh da ta’addancin su har abada. Yayi kira da jami’an tsaro da su kula da fararen hula kamar yadda ya kamata su kuma girmama hakkin dan adam.

An ga hayaki na tashi sararin samaniya a safiyar yau lahadi yayinda Jirgin yakin sojojin gamayyar Amurka ya kai hari wajen da yan tsagerun suke a Kudancin Mosul haka kuma Jami’amn Yansandan Iraqi dauke da makamai sun tun kari birnin, Yan sanda dake dauke da manya manyan makamai irin na sojoji sun shirya domin shiga Arewacin da manyan motocin yaki da ga tashoshinsu kudu da birnin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG