Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kashe Mutane Sama Da 70 Da Ake Zargin ‘Yan Ta’adda Ne


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Dakarun sojin Najeriya sun kashe mutane sama da 70 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a wani farmaki da suka kai a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Musa Danmadami, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin da yake yi wa manema labarai karin haske game da ayyukan da sojojin suka yi cikin makonni biyu da suka wuce.

Ya ce an kuma kama ‘yan ta’adda sama da 140 a tsawon lokacin, tare da kwato makamai da dama da suka hada da bama bamai hadin gida.

Gidan talabijin na Channels da ya rawaito mai magana da yawun hedikwatar tsaron na cewa mambobin kunigyar ISWAP sama da 500 ne suka mika wuya ga sojoji.

“Sojoji sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 40, tare da kama ‘yan ta’adda 25 da kuma 8 da ke samar da kayan aikin taaddanci. Sojojin sun kuma ceto fararen hula 131 da aka yi garkuwa da su, yayin da jimillar ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP 510 da iyalansu, da suka hada da manya maza 54, manya mata 164 da kananan yara 292 suka mika wuya ga sojoji a wurare daban-daban a cikin inda dakarun suka yi aiki,” a cewar Danmadami.

“Dukkan abubuwan da aka kwato, da wadanda ake zargin an mika su ga hukumar da ta dace domin ci gaba da daukar mataki. Hakazalika, an bayyana ‘yan ta’addan da aka kubutar da ‘yan ta’addan da suka tsere da iyalansu kuma ana kula da lafiyarsu, yayin da ‘yan ta’addan da suka mika wuya kuma an bayyana su domin daukar mataki na gaba.”

A halin da ake ciki kuma, rundunar sojin ta kuma tababtar da cewa an kubutar da biyu daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da aka sace a watan Afrilun 2014, baya ga wasu fararen hula sama da 150 da aka ceto a wasu hare-haren da sojoji suka kai a yankin arewa maso gabas.

XS
SM
MD
LG