Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Ceto Dalibar Chibok Da ‘Ya’yanta Uku


'Yan matan Chibok da aka sace
'Yan matan Chibok da aka sace

Sojojin Najeriya sun ceto wata mata da ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa da ita shekaru goma da suka gabata a lokacin da take yarinya 'yar makaranta a kauyen Chibok, in ji rundunar a ranar Alhamis. An kuma ceto 'ya'yanta uku.

Sojojin Najeriya sun kubutar da Lydia Simon mai dauke da cikin wata biyar a yankin karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno, inda aka shafe shekaru 15 ana ta da kayar baya da masu ikirarin jihadi, a cewar sanarwar da rundunar ta fitar. Hukumomin ba su fadi shekarunta ba, amma mai yiwuwa tana da shekaru 20.

Sanarwar na kunshe ne da hoton Simon da ‘ya’yanta, wadanda ake ganin suna tsakanin shekaru 2 zuwa 4. Ya zuwa yanzu dai ba ta riga ta hadu da ‘yan uwanta ba.

Simon na cikin 'yan mata 276 da aka sace daga makarantarsu da ke Chibok a watan Afrilun 2014 a lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula a yankin. Har yanzu kimanin 82 daga cikinsu na nan tsare a hannun mayakan.

Zanga-zangar neman a je a kubuto da dalibai mata na Chibok da 'yan Boko Haram suka sace a Abuja, Yuni 3, 2014.
Zanga-zangar neman a je a kubuto da dalibai mata na Chibok da 'yan Boko Haram suka sace a Abuja, Yuni 3, 2014.

A karon farko cikin jerin sace-sacen jama'a da aka yi a wasu makarantu a kasar Afirka ta Yamma, sace 'yan matan Chibok ya girgiza duniya tare da janyo wani kamfen na dandalin sada zumunta na duniya mai taken #BringBackOurGirls.

Rundunar sojin Najeriya ba ta bayyana yadda aka kubutar da ita ba, sai dai an ceto ta ne a wani wuri da ake kira Ngoshe, mai tazarar kilomita 130 (mil 74) arewa da babban birnin jihar Bornon Maiduguri.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG