Accessibility links

Mataimakin shagaban Sudan ta Kudu na farko, Taban Deng Gai yana kira ga kasashen duniya masu taimako da kada su yi watsi da kasar tashi a daidan wannan lakoci da da kasar ke cikin mawuyacin hali, na yawan yake-yake.

Haka kuma wannan sabuwar kasa ta duniya na huskantar kalubalolin kayan agaji, a yayin da dubban yan kasar suka gudu, suka yi hijira zuwa kasashen dake makwaptaka da ita don neman mafaka.

Deng ya fada jiya Alhamis a wurin taron MDD a New York, cewa halin da al’ummar kasar ke ciki na wahala ya wuce gona da iri.

Mataimakin shugaban na Sudan ta Kudu Deng ya kara da cewar yake-yake a wannan shekara a yankunan Wau, da Raja, da kuma Juba sun kara dagula al’amura.

Sai dai kuma ya dora laifi a kan ambaliyar da aka samu sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya wadda ta fid da mutane daga gidajensu a jihohin Upper Nile da kuma Bahr al Ghazal.

Duk da wannan hali da ake ciki, Deng yace hankali ya soma kwantawa a kasar ta Sudan ta Kudu.

An dai yi wani zaman tattaunawa a jiya Alhamis a wurin taron MDD a kan rikicin Suda ta Kudu da kuma kalubalolin da take fuskanta na kayan agaji.

XS
SM
MD
LG