Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tabarbarewar Tattalin Arzikin Najeriya ya Shafi Kasashen Irin Su Nijar


Wasu matasan Nijar dake zaman kashe wando, babu aiki sai shaye shaye
Wasu matasan Nijar dake zaman kashe wando, babu aiki sai shaye shaye

Tun lokacin da Najeriya ta samu kanta a wani hali na tabarbrewar tattalin ariki kasashen dake makwaftaka da ita su ma tattalin arzikinsu ya shiga wani hali na rabbana ya wadatamu

Kasashen dake makwaftaka da Najeriya irinsu Nijar sun shiga wani yanayi da basu saba dashi ba na tsadar rayuwa da rashin kudi da rashin aikin yi, musamman ga matasa.

Wannan lamarin na rashin aikin yi ga matasa ya sa iyayen matasan jamhuriyar Nijar suka kira matasan da gwamnati domin ta yiwa matasan dubi da idon basira domin samar masu abun yi.

Wani uban matashi yace suna son su jawo hankalin matasa da su tashi tsaye da kansu domin duniya ta canza. Ga tsadar rayuwa yanzu ta yiwa mutane yawa. Mutane na cikin matsaloli. Yace idan matashi bashi da abun yi sai wannan matsalar ta jawo wata. Yace suna jan hankalin gwamnati da tayi kokari ta samar ma matasa abubuwan yi.

A nasu bangaren matasan na cewa lallai da gaske ne ba'a yi dasu a harkokin yau da kullum. Suka ce a duk ayyukan gwamnati ba'a sa matasa ciki ba. An mayar dasu saniyar ware. Suna fata za'a basu zarafi su shiga harkokin gwamnati su bada tasu gudummawar.

Ga rahoton Mamma Haruna Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

XS
SM
MD
LG