Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Ta Jefa Kuri'ar Bai Daya Akan Biritaniya


Donald Tusk
Donald Tusk

An gudanar da taron ficewar Biritaniya daga Turai batare da Firaministan kasar Biritaniya ba

Kungiyar taraiyar turai ta jefa kuri’ar bai daya na yin na’am da tsari ko kuma ka’idodin da za’a bi wajen yin shawarwarin ficewar kasar Ingila daga cikin kungiyar. Donald Tusk shugaban taron kolin da kungiyar ke yi a birnin Brussells kasar Belgium shine ya baiyana haka a sakon daya sa cikin dandanlin tweeter sa yau Asabar.

Shugabanin kungiyar taraiyar turai suna yin taron kolin ba tare da Prime Ministar Ingila Theresa May ba.

Cikin kasa da mintoci goma sha biyar shugabanin kungiyar su ashirin da bakwai suka yi na’am da tsarin ko kuma ka’idodin.

Za’a fara tattaunawa da Ingila jim kadan bayan zaben da za’a yi a ranar takwas ga watan Yuni idan Allah ya kaimu

Tataunawar zata maida hankali akan harkokin kyautata rayuwa yan kasashen EU da iyalansu wadanda suke zaune a Ingila da kuma batun kudin da kungiyar ke bin kasar Britaniya. Domin kungiyar ta dage akan cewa tilas Ingila ta dauki jidalin biyan kudin janyewa daga cikin kungiyar da zai kai kimamin dala biliyan sittin da biyar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG