Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kungiyar Fulani Mabiya Addinin Krista a Jos


file photo.
file photo.

Al’ummar Fulani mabiya addinin Krista sun gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya a Najeriya da sauran sassan Duniya.

A taron na shekara-shekara da kungiyar Fulanin take gudanarwa a garin Jos, al’ummar fulanin da suka fito daga sassa daban-daban na Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Burki Na Faso da sauran kasashen Afirka, sun koyar da junansu muhimmancin nuna ‘kauna ga kowa da inganta zamantakewarsu da sauran al’umma.

Shugaban kungiyar Rev Buba Aliyu, yace dalilin taron shine su yi cudanya da ‘karfafa juna don yin sulhu da kowa. inda yace sun yiwa shugaban ‘kasa da gwamnatoci addu’o’i.

Mutanen da suka ziyarci wannan taro sun nuna gamsuwarsu da muhimmancin zaman lafiya a duniya. Ita dai kungiya Fulani mabiya addinin Krista ta kwashe shekaru 40 tana gudanar da al’amuranta.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG