Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Yace Akwai Masu Son Mukamin Mai Bada Shawara Akan Tsaro


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya shirya komawa bakin aikin sa na mulki, kwana daya bayan gudanar da gagarumin taron magoya bayansa a Florida inda ya kara Allah wadai da kafafen yada labaran da ya kira masu jabun labari.

Shugaban kasar ya shirya kashe ranar lahadi kacokan domin tattaunawa da wadanda yake son ayyanawa a matsayin mai bashi shawara kan harkokin tsaro.

Trump ya fadawa yan Jarida a cikin Jirgin saman Airforce One a jiya asabar cewa “Akwai mutane da yawa da suke son aikin” ya kara da cewa akwai wanda yake tunani tun kwani uku zuwa hudu da suka wuce, amma dai zamu ga abin da zai faru, zan tattauna da wannan mutumin. Gaba dayan su mutanen kwarai ne, kuma masu kima.”

A cikin wadanda ake sa ran zai gani kan abinda ya shafi matsayin sun hada da, Mai rikon kwarya Mai daba shawara kan harkokin tsaro Army. Lt. Gen. Keith Kellog Mai ritaya, da John Bolton, tsohon Jakadan Amurka a MDD, Army lt. Gen. H.R. McMaster, da kuma Sufurtanda makarantar sojoji ta West Point, Lt. Gen. Robert Caslen.

Haka kuma Trump ya shirya ganawa da shugabannin kasashen waje ta wayar tarho da kuma zaman tattaunawa kan Tsarin Harkar Lafiya.

A jiya Asabar din a yayin wani taron gangami mai kama da Kamfe , Trump ya bayyana gwamnatinsa na samu Cigaba na ban mamaki, amma yayi tsokaci akan abinda ya kira Kafafen tyada labarai na bada rahotanni na karya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG