Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kashe Sojoji A Ukraine Duk Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma


Shugaban Ukraine Petro Poroshenko yana magana da sojojin Amurka da suka kawo masa kayan yaki
Shugaban Ukraine Petro Poroshenko yana magana da sojojin Amurka da suka kawo masa kayan yaki

Bisa ga alamu yarjejeniyar da Ukraine da 'yan tawaye suka cimma ba zai dore ba domin ana cigaba da kashe sojojin Ukraine din tare da jikata wasu.

An kashe wani sojan Ukraine daya tare da jikaata wasu guda takwas a wani hari da aka kai gabashin kasar.a yayin da fada ya zafafa tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye dake samun goyon bayan Rasha duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka kulla.

Hare-haren jiya Lahadi sun auku ne kusa da birnin Donetesk wanda ya zama tamkar babban birnin 'yan tawayen.

Ko ranar Asabar ma Ukraine ta sanar cewa a kashe mata sojoji biyar a wani harin kaitsaye da 'yan tawayen suka kai.

A karkashin yarjejeniyar da suka cimma duka bangarorin biyu yakamata su janye makamansu daga bakin daga. Wannan na cikin matakai goma sha biyu da aka lissafa a cikin yarjejeniyar..

Idan ba'a manta ba a watan Maris din shekarar 2014 ne 'yan tawayen gabashin kasar ta Ukraine suka soma bori bayan da kasar Rasha ta hada yankin Crimea da kasarta daga Ukraine. Abun da Rasha ta yi shi ne 'yan tawayen suke so su yi, wato su balle daga Ukraine bayan da gwamnatin dake bin ra'ayin yammacin turai ta karbi mulkin kasar. Kawo yanzu kimanin mutane 8,000 suka rasa rayukansu a rikicin.

Ita dai kasar Ukraine da kasashen yammacin turai suna zargin Rasha da goyon bayan 'yan tawayen tare da basu makaman yaki. Amma Rasha ta musanta zargin.

XS
SM
MD
LG