Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

VOA Zata Ci Gaba Da Yada Shirye-Shiryenta Duk Da Takunkumin Da Hukumomin Burkina Faso Ta Kakaba Mata


Matakin da Hukumar ta CSC ta dauka ya hada da bada umarnin dakatar da sake yada rahoton nan take tare da dakatar da shirye-shirye kafafen yada labaran kasa da kasar 2 tsawon makonni 2.

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Burkina Faso (CSC) ta bada sanarwa game da dakatarwar wucin gadin data yiwa shirye-shiryen kafafan yada labaran BBC-Afrika dana Muryar Amurka (VOA) sakamakon yada wani sabon labari akan wani rahoton hukumar kare hakkin dan adam ta “Human Rights Watch” wanda ya zargi dakarun rundunar sojin Burkina Faso da taki hakkin farar hula.

Haka kuma, an dakatar da damar shiga shafukan yanar gizon kafafen yada labaran 2 na BBC da VOA harma dana hukumar kare hakkin bil adaman ta “Human Rights Watch a fadin kasar burkina faso,

A labarin data yada game da rahoton na Human Rights Watch, VOA ta nemi jin ra’ayin jami’an gwamnatin Burkina Faso da dama amma bata samu kowane irin martani ba.

VOA zata cigaba da yada shirye-shiryenta akan kasar Burkina Faso kuma ta kudiri aniyar cigaba da bada cikakkun rahotanni cikin gaskiya da adalci game da al’amuran dake faruwa a kasar.

"Muryar Amurka (VOA) ba zata fasa yada shirye-shiryenta akan Burkina Faso ba kuma ta kudiri aniyar cigaba da kawo rahotannin abubuwan dake faruwa a kasar cikin gaskiya da adalci", a cewar Daraktan VOA na Riko, John Lippman.

Ya cigaba da cewar, "Muryar Amurka na matukar biyayya ga ka'idojin yada sahihan rahotannin da suka baiwa kowane bangare hakkinsa tare da kiyaye cikakken tsarin aikin jarida, akan haka ne muke kira ga gwamnatin Burkina Faso da ta sake nazari akan matakin da ta dauka mai tada hankali".

Lippman ya kara da cewar, "a daidai lokacin da duniya ke shirye-shiryen gudanar da bikin Ranar Yancin 'Yan Yaridu ta Duniya mako guda daga yanzu, matakin baya-bayan nan na hana gudanar labarai da rahotanni cikin 'yanci wani misali ne daya bayyana gaskiyar dake kunshe a cikin taken Muryar Amurka na: " 'Yancin 'yan jaridu na da mahimmanci".

A wata hira da yayi da kafar yada labarai da harshen Faransanci ta Muryar Amurka, Shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta “Reporters Without Borders” mai kula da yankin kudu da hamadar saharar Afrika, Sadibou Marong, yace “muna ganin yadda batun ‘yancin fadin albarkacin baki ke kara tabarbarewa, kamar yadda aka gani a dakatarwar da aka yiwa kafafen yada labaran BBC da voa.

“A wurinmu, wannan dakatarwar cin mutunci ne kuma karara tauyewa al’umma ‘yancinsu ne na samun bayanai”.

A cewar Mr. Marong, “a koda yaushe haka ne dabi’ar hukumomin Burkina Faso. duk sa’ilin da kafafen yada labarai suka nemi jin ra’ayi ko matsayinsu game da wani abu, galibi basu cewa komai ko kuma su kirkiri dalilin da zai sa suki cewa komai din.”

Shima a nasa jawabin game da lamarin, babban mai bincike akan nahiyar Afrika na Cibiyar ‘Yan Jaridun Duniya (CPJ), Jonathan Rozen, yace “CPJ na ankare da cewar hukumomin Burkina Faso sun dakatar da kafafen yada labaran BBC Afrika da VOA daga yada shirye-shiryensu.

Wannan dakatarwar fadadawa ce akan salon hana ‘yan jaridu gudanar da ayyukansu yadda ya dace a kasar, abinda ya hada da dakatarwar da aka yiwa kafafen yada labaran kasar Faransa dama na kasar Burkina Fason da dama a baya.

A bisa kididdagar da aka gudanar a shekarar 2020, yawan masu sauraran Muryar Amurka a kowane mako ya kai kaso 14.3 cikin 100.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG