Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kamfanin Indiya da Gwamnatin Nijar Sun Shiga Takaddama Akan Kwangilar Buga Fasfo


Firayim Ministan Nijar Birji Rafini
Firayim Ministan Nijar Birji Rafini

Takaddamar tsakanin kamfanin Indiyan da gwamnatin Nijar ta samo asali ne daga matakin soke wata kwangilar buga fasfo da gwamnatin ta ba kamfanin amma daga baya kuma ta soke kwangilar.

Gwamnatin Nijar ta dauki matakin ne a shekarar 2011 saboda a cewar hukumomin kwangilat ta sabawa doka.

Kamfanin ya gurfanar da gwamnatin ta Nijar a gaban kotu wadda kuma ta ba kamfanin gaskiya. Amma duk da gaskiyar da kotun ta ba kamfanin hukumomin Nijar sai suka kafe kan bakarsu. Dalili ke nan da kamfanin ya kara shigar da kara a kasar Ivory Coast. Kara ta kai biranen Paris a kasar Faransa da Washington DC kasar Amurka.

Kotunan sun yiwa kasar Nijar kamuwar kudin ofishin jakadancinta dake Faranasa da wasu kudaden diyya biliyan goma sha shida ta sefa dake hannun kamfanin Ariva wadanda yakamata a yi anfani dasu wajen gyaran hanyoyin Agadez da Tawa da Ale. Sai kuma wani katafaren otel mai hawa shida mallakar Nijar dake birnin New York wadanda ake sa ran sayarwa domin biyan kamfanin Indiyan a zaman kotun Paris a watan gobe.

Wasu 'yan Nijar suna dorawa Firayim Ministan kasar laifin wannan takaddamar kodayake sakataren gwamnatin Nijar din yace zargin bashi da tushe.

Gwamnati ta ce rashin bin doka ya sa aka soke kwangilar. Tsadar fasfo din ma na cikin dalilin da ya sa aka soke kwangilar.

Souley Barma nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG