Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Mai Neman Shugabancin Najeriya Ne Yake Neman Bata Gwamna Shetima AYankin Kudu -Isa Gusau


Gwamnan Borno Kashim Shetima
Gwamnan Borno Kashim Shetima

Wannan makon aka fitar da wani faifai inda aka ce gwamnan Boron Kashim Shettima da gwamnan Ogun Amosun ne ke caccakar kabilar Igbo a yunkurin da su keyi na neman kasar Biafra.

Mai taimakawa gwamnan Borno kan labaru Isa Gusau yace faifan sauti da aka yada a yanar gizo dake nuna muryar gwamna Kashim Shettima ce da gwamna Ibikunle Amosun na Ogun inda suka caccaji 'yan kabilar Igbo ba gaskiya ba ne.

Isa Gusau yace wani mai neman takarar shugabancin Najeriya ne daga yankin arewa ya tsara sautin da zummar bata gwamna Shettima a yankin kudancin Najeriya.

Inji Isa Gusau sun san mutumin amma yanzu ba zasu bayyana sunansa ba har sai shekara ta 2019. Amma yace gwamnan Borno bai taba cewa yana neman shugabancin Najeriya ba.

Sautin ya bayyana Shettima da Amosu na koyin Sultan Sa'ad Abubakar III da Shugaba Buhari da kuma Rotimi Amaechi. Gusau yace wanda ya kawaikwayi Shettima ya manta Shettiman nada lankwasar harshe irin na Kanuri. Yana kuma magana a hankali ne ba da sauri ba.

Wasu da aka zanta dasu sun ce muryoyin da suka ji basu yi kama da na Shettima ko Amosun ba.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG