Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasikar Tsohon Shugaba Obasanjo ta Tayar da Kura


Tsohon shugaban Najeriya Olusegub Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegub Obasanjo

Jiya kafofin labarai a Najeriya suka bayyana wasikar da tsohon shugaba Obasanjo ya rubutawa shugaba Jonathan mai shafi 18 a bainar jama'a inda ya tabo batutuwa da yawa kuma masu mahimmanci

Cikin wasikar da tsohon shugaban kasa ya rubutawa shugaba Goodluck Jonathan mai shafi 18 ya tabo matsalolin da suka addabi kasar da kuma irin rawar da gwamnatin yanzu ke takawa.

Chief Olusegun Obasanjo ya tunawa shugaba Jonathan alkawarin da ya dauka a lokuta daban-daban cewa wa'adi daya kawai zai yi na shugabanci kana ya mikawa arewa. Ya jawo hankalin shugaban ga irin siyasar da ake yi yanzu wadda kamar gwamnatin ta kabilar Ijaw ce kawai, wato kabilar shi Jonathan. Ya fada masa cewa 'yan Najeriya daga sassa daban daban suka zabeshi. Kabilar Ijaw kawai bata isa ta dora shi kan mulkin Najeriya ba. Kana kuma ga batun tabarbarewar tsaro a kasar musamman a arewa maso gabas. Gwamnati ta gaza kawar da barazanar kungiyar Boko Haram.

A cigaba da bayani Obasanjo ya ce shugaba Jonathan yana mulkin yadda ya raba kawunan 'yan kasar tsakanin Musulmai da Kirista kuma tsakanin kudu da arewa. In ji Obasanjo wannan irin mulkin zai kai ga hallaka kasar lamarin da ka iya kashe mulkin dimokradiya ya dawo da sojoji. Wani abu kuma mai sosa rai da Obasanjo ya ambata shi ne yadda na kusa da shugaba Jonathan ke tafka muguwar satar kudin gwamnati da kadarorinta da ba'a taba gani a kasar ba. Tsohon shugaban ya bada wasu alkaluma masu ban tsoro dangane da sace-sacen da ake yi karkashin shugaba Jonathan.

Wasikar ta tsohon shugaba Obasanjo ta tayar da kura. Jama'ar Najeriya sun soma mayar da martani. A jihar Adamawa mutane da dama sun fadi albarkacin bakinsu. Alhaji Ahmed Lawal na wata kungiya da ta taimaka wurin zaben shugaba Jonathan a zaben 2011 ya ce wasikar ta dace sabo da a matsayin Jonathan na shugaba idan yana abun da ba daidai ba yakamata a jawo hankalinsa. Bai kamata a bar shugaba yana kaucewa hanya ba kuma mutane su yi shiru. Duk wanda ya ce gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba. Jonathan bashi da masoya da suka wuce wadanda ke fada mashi gaskiya.

To saidai mutane kamar su David Bata suna ganin matakin da Obasanjo ya dauka bai dace ba. Bai kamata ya rubuta masa wasika ba. Da kiransa ya yi ya bayyana masa abubuwan da ya hango. Shi kuma dan siyasa Huseini Gambo ya ce masu ba shugabanni shawara su suke haddasa masu matsaloli, su kai shugaba su baro. Ya ce basu bashi shawara nagari. Yana ganin ana anfani da masu bashi shawara domin a wargaza masa mulki domin ya fadi gaba daya.

Shi kuma mai baiwa shugaban kasa shawara Reuben Abati ya ce wasikar wata dabara ce ta harzuka 'yan Najeriya. Ya ce shugaban da kansa zai mayar da martani a kan wasikar da ya ce bata da tushe bare makama.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG