Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Falasdinawa Sun Shigar Da Karar Gwamnatin Biden


Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden.

Wasu iyalan Falasdinawa biyu a Amurka sun shigar karar gwamnatin Biden, suna masu cewa gwamnatin ba ta yi wani abu ba wajen kwashe ‘yan uwansu Amurkawa da suka makale a Gaza kamar yadda ta yi wa ‘yan Isra’ila kuma Amurkawa.

A kwanakin baya bayan harin da kungiyar Hamas ta kai a kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, gwamnatin Amurka ta shirya jiragen haya daga Tel Aviv zuwa Turai, domin taimakawa Amurkawa barin Isra'ila bayan da kamfanonin jiragen sama da dama suka soke zirga-zirga a kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce ta taimaka wa Falasdinawa kusan 1,300 na Amurka ficewa daga Gaza, tare da tserewa harin ramuwar gayya da Isra'ila ke yi - a wani bangare ta hanyar daidaita ficewarsu zuwa makwabciyarta Masar tare da hukumomin Isra'ila da Masar.

Sai dai Amurka ba ta dauki matakin shirya jiragen da aka kebe ba ko kuma ta taimaka wajen tabbatar da ficewar wasu Amurkawa kimanin 900 mazauna yankin da 'yan uwa da ke ci gaba da makale a Gaza, in ji iyalan Amurkawa da ke karar gwamnati.

Sun ce hakan ya sabawa ‘yancin da tsarin mulkin da kasar ya ba su.

kamfanin dillancin labaru na Reuters ne ya hada wannan rahotan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG