Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata a Sauke Shugaba Kiir - Janar Swaka


Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir

Wani Janar din kasar Sudan ta Kudu da ya sauya sheka, ya zargi shugaba Salva Kiir cewa yana bata kasar kuma lokaci ya yi da za a kawar da gwamnatinsa.

Janar Thomas Cirillo Swaka, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Muryar Amurka a wata mabuya da ba a bayyana ba, jim kadan bayan da ya kaddamar da wata sabuwar kungiyar ‘yan tawaye mai suna National Salvation Front.

A cewar Janar Swaka, Shugaba Kiir yana ta kashe mutanen kasar tare da cin amanarsu da kuma dishe masu burinsu, saboda haka ya zama dole ‘yan kasar su fito kwansu da kwartarsu su ga cewa sun sauke shi daga mulki.

Sudan ta Kudu dai ta fanjama cikin kangin yakin basasa ne, tun bayan da fada ya barke tsakanin masu goyon bayan shugaba Kiir da kuma masu adawa da mulkinsa a shekarar 2013.

Wannan fada ya raba sama da mutane miliyan biyu da muhallansu kana ya haifar da matsalar karancin abinci a wasu sassan kasar.

A watan Disambar shekara 2013 rikici tsakanin shugaba Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar ya barke, bayan da Kiir ya zargi Machar da wasu mutane goma da yunkurin yi mai juyin mulki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG