Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Firgita Masu Sallar Tahajjud Lokacin Da Suka Kai Wani Hari Garin Gusau


Wasu masallata suna sallah a Masallaci
Wasu masallata suna sallah a Masallaci

Masu ibada a wani masallaci da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, sun tsere a ranar Talata a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka far wa mazauna yankin.

WASHINGTON, D. C. - ‘Yan bindigan dai sun fara shiga gidan wani dan kasuwa ne inda suka kashe shi kafin su yi awon gaba da matarsa da makwabcinsa. An harbe mutumin ne saboda ya ki tafiya da maharan.

A cewar wani makwabcin marigayin, Alhaji Jafar, an harbe Nagoma ne a ciki kuma aka garzaya da shi asibitin Sarki Fahad inda ya rasu a lokacin da ake jinya.

Jafar ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun mamaye al’ummar garin ne da misalin karfe 1 na safe, inda suka nufi gidan Alhaji Nagoma, wanda kuma shi ne manajan kamfanin mai na Raheem Petroleum, inda suka yi yunkurin yin garkuwa da shi.

“Lokacin da ‘yan fashin suka gane cewa mutumin ba zai yi kasa a gwiwa ba, sai suka harbe shi a ciki suka yi awon gaba da matarsa. Aka bar shi yana kururuwa don neman taimako yayin da 'yan fashin suka ci gaba da harbe-harbe kai tsaye."

Wani mazaunin gidan mai suna Aminu Musa ya ce a gida na biyu ‘yan fashin sun kuma yi yunkurin yin garkuwa da wasu ma’aurata, amma mijin ya roke su da su bar matarsa saboda tana da juna biyu.

"Matar tana da juna biyu kuma bayan mijin ya roki 'yan fashin, sai suka bar ta amma suka tafi da shi."

Ya kara da cewa a dai-dai lokacin ne wasu ‘yan kungiyar ‘yan banga suka yi yunkurin dakile harin amma ‘yan bindigan suka ci gaba da harbe-harbe ta ko ina, inda suka hana ‘yan banga tunkararsu.

“Yayin da ‘yan bindigan ke ci gaba da harbe-harbe a lokacin da suke ficewa daga cikin al’umma, wasu masu gudanar da Sallar Tahajjud cikin tsoro suka bar masallacin suka tsere. Dalilin haka ne mutane da yawa suka zata masallacin aka kai wa hari. Amma gaskiyan shine ‘yan fashin ba su kai hari masallacin ba.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Shehu Muhammad Dalijan, wanda ya tabbatar da kashe ‘dan kasuwar da kuma sace wasu mutane biyu ya musanta kai hari akan masallacin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG