Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 3 Tare Da Yin Garkuwa Da Wasu 8 A Jihar Kaduna


Yan bindiga
Yan bindiga

Harin na baya-bayan nan na zuwa ne kwanaki 5 bayan da ‘yan bindigar suka hallaka mutane 23 a anguwan danko ta yankin dogon dawa dake gabashin karamar hukumar Birnin Gwari.

WASHINGTON DC - ‘Yan bindiga sun sake hallaka akalla mutane 3 tare da yin awon gaba da wasu mutum 8 a wani sabon hari da suka kai kan gundumar Kakangi dake kauyen Hayan Habuja na karamar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna.

Har yanzu hukumomin ‘yan sanda da gwamnatin jihar Kaduna basu ce komai akan al’amarin ba.

Saidai, Babban Sakatare a kungiyar Cigaban Masarautar Birnin Gwari, Abdurrashid Abarshi ya shaidawa tashar talabijin ta Channels cewar ;yan bindigar sun afkawa kauyen ne da misalin karfe 3 na yammacin jiya Talata, bayan da suka yi sansani a wani wuri dake kusa a daren Litinin domin kammala tsare-tsaren aiwatar da harin.

Yace ‘yn bindigar sun harbe mutane 2 nan take sa’annan suka yi awon gaba da wasu mutanen 4.

Ya kara da cewar, akan hanyarsu ta zuwa kauyen Hayan Habuja, ‘yan bindigar sun sake hallaka wani mutumin kauye dake tattara itace sannan suka yi garkuwa da wasu karin mutum 4.

A sanarwar data fitar biyo bayan karuwar yawan hare-hare, kungiyar Cigaban Masarautar Birnin Gwari, ta bukaci hukumomin da al’amarin ya shafa dasu tsananta tare da gaggauta daukar matakan kawo karshen barazanar tsaron da taki ci taki cinyewa.

Kungiyar ta kara da cewar al’ummar Birnin Gwari na rayuwa cikin tashin hankali, inda ta jaddada bukatar inganta matakan tsaro domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG