Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama a Kauyukan Sokoto


Yan bindiga
Yan bindiga

'Yan bindiga na ci gaba da cin karensu ba babbaka a wasu yankunan arewacin Najeriya duk da kalaman da mahukunta ke yi na cewa suna daukar matakai na magance matsaloin.

Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin wuraren da 'yan bindiga ke zafafa kai hare-hare, musamman a gabascin jihar.

Wasu mazauna yankunan da matsalar rashin tsaro ke addaba sun ce har yanzu lamarin bai sauya ba, domin a ko da yaushe basu samun bacci da idanu biyu a rufe.

Yankunan karamar hukumar Goronyo na daga cikin wuraren da lamarin ya fi kamari a kwanannan, domin kusan kullum sai an samu rahoton kai hari a yankin.

Yan bindiga
Yan bindiga

A karshen makon da ya gabata an samun rahoton kai hari a garin Takakume, bayanai sun nuna cewa an kashe mutane 6 sannan aka yi garkuwa da wasu mutum 15.

Bashir Altine Guyawa shi ne shugaban rundunar adalci, na daga cikin masu bibiyar lamarin rashin tsaro a Najeriya, ya ce dukkan hare-haren da ake kai wa gabashin jihar Sokoto ba daga bakin barayi bane.

Ko a ranar Ladadi an wayi gari da labarin hari a garin Kwakwazo duk a karamar hukumar ta Goronyo. A hirarsa da Muryar Amurka, Dangaladimam Kwakwazo Nasiru Galadima, ya ce mutane na zaune ne kawai sai suka ga barayi sun far musu, suka dinga harbe-harbe har mutane suka tarwatse sannan suka dinga bi gida-gida suna kama mutane.

Duba da yadda 'yan bindiga ke zafafa kai hare-hare a yankunan gabashin Sokoto ya sa masu bibiyar lamari a yankin ke ganin kamar akwai bakin barayi da ke shiga yankin suna addabar jama'a, kamar yadda Bashir Altine Guyawa ya bayyana.

Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin rundunar 'yan sanda a jihar, sai dai kakakinta ASP Ahmad Rafa'i ya shaida cewa baya gari.

Hakazalika, nan take bangaren gwamnati ma bai ce komai ba, amma a wata ganawa da muryar Amurka ta yi da Mataimaki na musamman ga gwamna akan lamarin tsaro kanal Abdul A Usman mai ritaya a kwanannan, yace suna kan kokarin kafa rundunar tsaro da zasu yi aiki da ita wajen samar da zaman lafiya a fadin jihar.

Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da gurgunta arewacin Najeriya duk da yake mahukunta suna kallon yadda matsalar ke fadada, sai dai sun fake da cewa suna daukar matakai, kuma wasu lokuta suna cewa suna samun galaba.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG