Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya Sun Sa Ido Su Ga Yadda Za Ta Kaya Tsakanin Hukumar EFCC Da Yahaya Bello Da Ya Tsere


Tsohon Gwamna Yahaya (Instagram/officialgybkogi)
Tsohon Gwamna Yahaya (Instagram/officialgybkogi)

Al’ummar jihar Kogi a Najeriya da masana kundin tsarin mulkin kasar na ci gaba da yin tsokaci akan dambawar dake tsakanin tsohon Gwamnan jihar Alhaji Yahaya Bello da hukumar EFCC.

KOGI, NIGERIA - Hukumar ta EFCC dai ta chafke Yahaya Bello ne a gidansa dake Abuja bisa zargin yayi sama da fadi da Naira biliyan 84 lokacin da yake Gwamnan jihar Kogi.

Rahotanni dai sun nuna cewa Yahaya Bello ya kubucewa hukumar ta EFCC ne bisa gudummuwar da ya samu daga Gwamnan na Kogi mai ci Usman Adodo.

A hirar shi da Muryar Amurka, Shugaban jam’iyyar APC a Lokoja Alhaji Maikudi Bature ya ce babu wani laifi da Yahaya Bello yayima ‘yan jihar Kogin sai dai masu yi mashi bita da kulli irin ta siyasa.

Masana kundin tsarin mulkin kasar na ganin lamarin dake tsakanin EFCC da Yahaya Bello akwai bukatar yin takatsantsan.

Da ya ke tsokaci game da lamarin, barista Mainasara Kogo Umar lauya mai zaman kansa a Najeriya ya ce hatta matakin da Gwamnan Usman Adodo ya dauka karan tsaye ne ga kundin tsarin mulkin Najeriya.

A yanzu dai al’ummar jihar Kogin dama sauran ‘yan Najeriya na ci gaba da zuba idanu domun ganin yadda za a kwashe tsakanin tsohon Gwamnan Kogin Yahaya Bello da kuma hukumar ta EFCC.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG