Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takarar Shugabancin Kasar Faransa Sun Tafka Muhawara Mai Zafi.


'Yan Takarar Shugabancin Kasar Faransa Marine Le Pen Daga Hagu Emmanuel Macron Daga Hagu.
'Yan Takarar Shugabancin Kasar Faransa Marine Le Pen Daga Hagu Emmanuel Macron Daga Hagu.

‘Yan takarar shugabancin kasar Faransa Marine Le Pen da Emmanuel Macron sun tafka muhawara mai zafi wadda aka nuna a gidan talabijin jiya Laraba, ‘yan kwanaki kafin a yi zaben gama gari a kasar.

Mrs. Le Pen ta bayyana abokin adawarta a matsayin rikakken dan jari hujja wanda ke da rauni wajen yaki da ta’addanci, shi kuma ya kira Marine din a matsayin makaryaciya mai tsattsauran ra’ayi.

A jawabin ta na farko lokacin muhawarar, Le Pen ta kira tsohon ministan harkokin tattalin arzikin a matsayin “dan takara mai ra’ayin “kowa yayi abinda yake so”.

Rashin ayyuka a kasar na cikin abubuwan da ‘yan takarar suka tattauna. Macron ya yi kira akan a saukaka ka’idojin gwamnati da na kanana da kuma matsakaitan sana’o’i, ita kuma Le Pen ta yi alkawarin zata kara haraji akan kayayyakin kamfanonin kasashen ketare.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG