Accessibility links

'Yan Tsageran Boko Haram Sun Mamaye Madagali

  • Grace Alheri Abdu

Wadansu mutane suna kallon barazunan gine gine bayan harin Boko Haram.

Wadansu mutane suna kallon barazunan gine gine bayan harin Boko Haram.

Rahotanni sun ce a yanzu haka ‘yan tsageran Boko Haram sun fara mamaye yankunan Madagali mai makwabtaka da jihar Adamawa.

Kwanaki hudu bayan kwace makarantar horas da zaratan ‘yan sanda dake Limankara a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno, rahotanni sun ce a yanzu haka ‘yan tsageran Boko Haram sun fara mamaye yankunan Madagali mai makwabtaka da jihar Adamawa.

A cikin hirarsu da wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz, wadansu mazauna garin Madagali, wanda ke dab da bakin iyakar Borno da Adamawa, kuma mai tazarar kilomita 20 kacal da Gwoza, sun ce sun ga mayakan Boko Haram cikin motoci sun fara kewayewa da mamaye wadansu kauyuka.

Shaidun suka ce, jami’an tsaro kalilan da suke wurin sun arce da isowar mayakan abinda ya tilasa mazauna kauyen suma kaura da neman ceton rayukansu.

Shima a cikin bayaninsa, shugaban karamar hukumar Madagali James Wartadda ya tabbatar da lamarin ya kuma ce jami’an tsaro basu da wani tasiri a wurin.

Ga cikakken rahoton Ibrahim Abdul’aziz.

XS
SM
MD
LG