Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar Yara Mata Ta Majalisar Dinkin Duniya


Malam Isa Suleiman tare da 'yan yara mata da yake taimakawa suna koyon sana'o'i maimakon auren dole na wuri kafin su cika shekaru goma sha takwas
Malam Isa Suleiman tare da 'yan yara mata da yake taimakawa suna koyon sana'o'i maimakon auren dole na wuri kafin su cika shekaru goma sha takwas

Ranar goma sha daya ta watan Oktoban duk shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya, ko MDD a takaice, ta kebe domin tunawa da yin nazari a halin da 'yan yara mata masu shekaru goma zuwa sha biyar suke ciki a duniyar nan tamu.

Wani kalubale da 'yan mata masu shekaru goma zuwa goma sha hudu da suke karo dashi shi ne tilasta masu yin aure da wuri da iyayensu sukan yi.

A wani bincike da aka yi an gano cewa kasar Nijar ce tafi aurar da 'yan mata tun shekarunsu basu kai ba lamarin da sau tari yakan haddasa cutar yoyon fusari ko VVF a takaice.

Hafsatu yarinya ce mai shekaru goma sha hudu dake jihar Maradi wadda ta gujewa auren wuri. Ita dai Hafsatu kin auren tayi tana cewa sai ta kai shekaru goma sha takwas domin ta samu sana'ar yi. Ta koyi sana'ar dinki kuma ta iya.

Hafsatu ta koyi yin dinki
Hafsatu ta koyi yin dinki

Isa Suleiman jami'i ne a ma'aikatar dake kula da yara mata da rayuwar mata a jihar Maradi. Ma'aikatar tana fadi ka tashi wajen ganin ba'a aurar da yaran da shekarunsu basu kai ba. Malam Isa yakan tattauna da iyayen dake kokarin aurar da 'ya'yansu yara mata tun shekarunsu basu kai ba. Yana wayar masu da kawuna akan illar yin hakan.

Sabili da bayanan da Isa Suleiman ya yiwa iyayen Hafsatu ya sa suka fasa aurar da ita yanzu sai ta kai akalla shekaru goma sha takwas.

Aikin Isa ya taimakawa Hafsatu da kawayenta da su ma yanzu maimakon su yi auren sauri suna koyon sana'o'in tunda iyayensu basu sasu makarantar boko ba. Ma'aikatar Isa ke daukan nauyin sana'o'in da yaran ke koyo tare da basu kayan aiki idan sun gama.

Ga rahoton Tamar da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

XS
SM
MD
LG