Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Shugaba Buhari Zai Kaddamar da Shirin Tsaftace Muhallin Yankin Ogoni A Rivers


Shugaba Buhari na Najeriya
Shugaba Buhari na Najeriya

Shirye-shirye sun kammala a jihar Rivers dangane da ziyarar Shugaba Muhammad Buhari ta yini daya a jihar domin kaddamar da shirin gyaran muhallin yankin Ogoni waanda an yi shekara da shekaru babu gwamnatin Najeriya da ta kula duk da rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta sha fitarwa a kai tare da gargadin a yi hakan.

Yankin dai na Ogoni ya gurbace shekara da shekaru sakamakon ayyukan hakan danyan mai da aka sha yi shekaru da dama.

Wanna ziyarar shugaba Muhammad Buhari tana zuwa ne a daidai lokacin da 'yan kungiyyar tsagerun Niger Delta da suke kiran kansu Niger Delat Avengers ko NDA ke tsananta kai hare-hare ga kamfanonin mai tare da yiwa lafiyar shugaban barazana. To saidai duk bangarorin tsaron kasar sun tsaya tsaf domin ganin ziyarar ta gudana lafiya.

Mai magana da yawun 'yansandan jihar Rivers DSP Ahmed Kidaya Muhammad yace suna shirye kan ziyarar shugaban kasa kuma sun tattauna da duk wadanda ya kamata su tattauna dasu akan ziyarar. Baicin shirin da 'yansandan suka yi akwai kuma goyon bayan sojoji.

Yace abubuwan dake faruwa a jihar Delta basa faruwa a jihar Rivers. Ke nan su basa fuskantar wata barazana daga koina.

An dade ana tafiyar hawainiya akan gyaran muhallin yankin Ogoni. Ko Majalisar Dinkin Duniya ma ta gargadi a gaggauta gyaran muhallin amma sai yanzu da gwamnatin Buhari ta zo ta mayar da hankali kai.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG