Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Shugaba Tinubu Zai Kai Ziyarar Aiki Kasashen Netherlands Da Saudi Arabia


Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban kasar zai kuma halarci taron tattalin arzikin duniya da aka shirya gudanarwa a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Afrilu a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

WASHINGTON, D. C. - A wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Litinin, ya ce, “Bisa gayyatar da Firaministan kasar Netherlands, Mark Rutte ya yi masa, shugaba Tinubu zai yi tattaunawa masu muhimmanci da Firaministan, sannan zai shiga taruka daban-daban tare da Mai Martaba, Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima ta Masarautar.

“Yayin da yake kasar Netherlands, shugaba Tinubu zai halarci taron kasuwanci da zuba jari na tsakanin Najeriya da Holland wanda zai hada shugabannin kungiyoyi da kungiyoyi a kasashen biyu don gano damammaki na hadin gwiwa, musamman a fannin noma da kula da ruwa wajen samar da sabbin hanyoyin samar da mafita mai dorewa ga ayyukan noma.

"Za a kuma tattauna sosai da jami'an Holland game da ayyukan sarrafa tashar jiragen ruwa wadanda a duniya ma an san su da kwarewa akai.

“Bayan tafiyarsa Netherlands, shugaban zai ci gaba da halartar wani taro na musamman na tattalin arzikin duniya (WEF) wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 28-29 ga Afrilu a Riyadh, Saudi Arabia.

“A taron tattalin arzikin duniya, wanda ya mayar da hankali kan Haɗin gwiwar Duniya, Ci gaba da Makamashi don Ci gaba, Shugaba Tinubu da mukarrabansa za su yi amfani da damar taron na sama da shugabanni 1,000 daga ‘yan kasuwa, gwamnati, da jami’o’in ilimi don shiga tattaunawa don ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci, ajandar sabunta kyakkyawan fata ga kasar."

Shugaba Tinubu zai samu rakiyar wasu ministoci da wasu manyan jami'an gwamnati.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG